- Majalisar dokokin Osun ta sake jaddada aniyar ta na kawar da bangaren shari’a daga cikin halin da take ciki na cin hanci da rashawa
- Majalisar tayi watsi da cewa ba gaskiya ba ne cewa matakan da aka dauka kan CJ na da nasaba da muradun siyasa
- Kafin Hakan dai mambobin Kungiyar Ma’aikatan Shari’a Ta Jihar sun Ayyana tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Majalisar dokokin jihar Osun ta sake jaddada aniyar ta na kawar da bangaren shari’a daga cikin halin da take ciki na cin hanci da rashawa.
Majalisar ta kuma jaddada cewa kudurin da ta yanke kan babban alkalin alkalai na jihar, Mai shari’a Oyebola Adepele Ojo, na janye shi daga gefe ya yi daidai da tsarin gaskiya da adalci.
KARANTA WANNAN: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Ministan Ciniki Kan Tallafin N250bn Na Gwamnatin Tarayya
Majalisar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da ta karbi bakuncin mambobin kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya JUSUN a harabar majalisar.
‘Yan kungiyar ta JUSUN sun kasance a Majalisar a ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da CJ da ke damun ta da kuma yadda take tafiyar da harkokin shari’a na jihar.
Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin shari’a, Kanmi Ajibola, wanda ya yi jawabi ga ma’aikatan shari’ar da suka yi zanga-zangar a madadin majalisar, ya ce matakin majalisar an yi shi ne domin tsaftace bangaren shari’a da cin hanci da rashawa domin dawo da kwarin gwiwar jama’a.
Ajibola ya yi watsi da cewa ba gaskiya ba ne a wasu bangarorin cewa matakan da aka dauka kan CJ na da nasaba da muradun siyasa.
Ya yi nuni da cewa bangaren samar da doka yana da aikin da kundin tsarin mulki ya dora masa na gudanar da ayyukan sa ido kan sauran bangarorin gwamnati guda biyu.
“Mun yaba da kasancewar ku a nan. Kuma akwai kwamitin da ke zaune kan wasu koke, wadanda mu mambobi ne. Don haka, ka same mu ne za mu jagoranci abin da za a ce a wannan dandali,” in ji shi.
“Amma bari in bayyana karara, mun samu wasu kararraki a kan CJ, kuma akwai rahotannin da ke rakiyar wadannan koke-koken da ke cewa idan har aka bar CJ ta shiga ofishinta, akwai wasu takardu da za a yi wa magudi, wadanda za su gurbata binciken.
Da suke jawabi tun da farko ’yan kungiyar ta JUSUN karkashin jagorancin shugaban su, Oluwagbemiga Eludire, sun ce sun je majalisar Dokokin Osun ne domin neman goyon bayan bangaren gwamnati domin ceto su daga rashin adalcin da CJ ke yi musu.
Yayin da yake karin bayani game da cin zarafin ofis da kuma rashin mutunta hakkinsu na ma’aikata da CJ ta yi, Eludire ya bayyana cewa, CJ ta tilasta wa kanta shiga harabar babbar kotun da safiyar Laraba tare da goyon bayan ‘yan sanda, inda suka fesa barkonon tsohuwa tare da yin harbi don tsorata ‘yan kungiyar ta JUSUN kai tsaye.
A wani labarin kuma, Zaben Gwamnan Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukaci Dawo da Kwafin hukuncin da Aka Yanke Domin Gyara
Bayan rudanin da ya biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamnan Kano, kotun ta bukaci lauyoyin da abin ya shafa da su mayar da kwafin hukuncin
Tuni bayan Hukuncin kotun ta bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris
A makon jiya ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori gwamnan Kano, Abba Yusuf, inda ta ce gwamnan bai cancanci tsayawa takara ba.
Bayan rudanin da ya biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamnan jihar Kano, kotun ta bukaci lauyoyin da abin ya shafa da su mayar da kwafin hukuncin da ta yanke domin gyara, Daily Post ta rahoto.
Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Laraba.