- Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Paul Merson, ya yi hasashen sakamakon wasannin gasar Premier a wasan mako na 13 da za a yi a filayen wasa daban-daban a kasar Ingila
- Tuni hasashen shahararren Dan wasan ya nuna yadda Wasu Mayan kungiyoyin wasa zasu Sha Kashi
- Tuni Wasu Daga Cikin kungiyoyin kwallon kafa suka daura Damarar Ganin wannan hasashen ya zamar musu gaskiya
Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Paul Merson, ya yi hasashen sakamakon wasannin gasar Premier a wasan mako na 13 da za a yi a filayen wasa daban-daban a kasar Ingila a karshen wannan makon da kuma daren Litinin.
Manchester City za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan farko na gasar Premier da yammacin ranar Asabar a filin wasa na Etihad.
KARANTA WANNAN: Hukumar Kwastam ta Mika Wa NDLEA Haramtattun Muggan Kwayoyin Da ta Cafke
Newcastle United za ta karbi bakuncin Chelsea a yammacin ranar Asabar, yayin da Arsenal za ta kara da Brentford.
Everton za ta kara da Manchester United ranar Lahadi, yayin da Tottenham Hotspur za ta kara da Aston Villa.
A cewar Sportskeeda, hasashen Merson Zai kasance kamar haka:
Manchester City zata lallasa Liverpool daci 2-1
Sheffield United zata lallasa Bournemouth daci 2-1
Nottingham Forest zata lallasa Brighton & Hove Albion da ci 2-1
Burnley zata ci West Ham United 1-0
Luton Town zata yiwa Crystal Palace ci 1-0 Mai ban haushi.
Newcastle United zasu tashi cancaras da Chelsea 1-1
Brentford zata Kashi da ci 1-3 a hannun Arsenal
Tottenham Hotspur zasu tashi cancaras da Aston Villa da ci 1-1
Everton zata ci Manchester United 2-1
Fulham itama zasu kare wasan da Wolverhampton Wanderers da ci 1-1
A wani labarin kuma, Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnan Kogi ta Sanya Lokacin Fara Zama
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kogi, karkashin jagorancin ta shirya fara zama a ranar Asabar Mai zuwa
Wannan dai Na zuwane bayan da Ododo na jam’iyyar APC ya lashe zaben ranar 11 ga watan Nuwamba da kuri’u 446,237
Sai dai bayan Shan Kaye da babban abokin hamayyarsa Ajaka na jam’iyyar SDP ya Yi ya samu kuri’u 259,052 inda ya Garzaya kutu
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kogi, karkashin jagorancin shugabar kotun daukaka kara (COA), mai shari’a Monica Bolna’an-Dongban, ta shirya fara zama a ranar Asabar.
Mista David Umar-Mike, sakataren kotun ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Lokoja ranar Alhamis.