- Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Sanata Uba Sani a matsayin zababben gwamnan jihar Kaduna
- Kafin Hakan dai dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, ya kalubalanci nasarar Uba Sani a kotu
- A baya dai kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna ta soke nasarar zaben gwamna Uba Sani
Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Juma’a ta tabbatar da zaben Uba Sani a matsayin zababben gwamnan jihar Kaduna.
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna ta soke nasarar zaben gwamna Uba Sani.
KARANTA WANNAN: Kotun Daukaka Kara ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi, ta Bada Umarnin Sake Sabon Zabe
Isah Ashiru, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, ya kalubalanci nasarar Sani a kotu.
Hakazalika, wani sashe na kotun daukaka kara dake zamanta a Legas ita ma ta tabbatar da zaben Francis Nwifuru a matsayin gwamnan jihar Ebonyi.
Kwamitin mutum uku ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a.
A wani labarin kuma, NNPCL Ya Sanya Ranar da Zai Kawo Karshen Shigo da Tace Man Fetur Daga Kasashen Waje
Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya ce za a kawo karshen shigo da taceccen man fetur zuwa kasar nan Nan da karahen watan Disambar 2024
NNPCL zai bunkasa kudaden shiga zuwa zunzurutun kudi Naira tiriliyan N4.5tn a karshen shekarar 2023
Hakan zai haifar da faduwa mai yawa a farashin kayayyakin man da aka tace
Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya bayyana cewa za a kawo karshen shigo da taceccen man fetur zuwa kasar nan Nan da karahen watan Disamba 2024.
A hasashen da NNPCL ya yi, kamfanin mai na kasa zai bunkasa kudaden shiga zuwa zunzurutun kudi Naira tiriliyan N4.5tn a karshen shekarar 2023, inda ya kara da cewa za a kammala gyaran matatar mai ta Fatakwal, a karkashin jagorancin NNPC a watan Disamba na wannan shekara.