- Kotun daukaka kara da ke Legas a wani hukunci da ta yanke, ta tabbatar da sake zaben Prince Dapo Abiodun a matsayin zababben gwamnan Ogun
- Alkalin kotun ya yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP ya shigar na kalubalantar Nasarar Abiodun
- Sai dai bayan Yanke Hukuncin Alkalin kotun ta bayar da umarnin sake sabon Zabe
Kotun daukaka kara da ke Legas a ranar Juma’a a wani hukunci da ta yanke, ta tabbatar da sake zaben Prince Dapo Abiodun a zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023 a matsayin zababben gwamnan Ogun, Punch ta rahoto.
Hukuncin mafi rinjaye da mai shari’a Joseph Shagbaor Ikyegh ya yanke ya yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu ya shigar a zaben gwamna na 2023.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani Ya Yaba da Hukuncin kotun Daukaka Kara
Sai dai kuma hukuncin da ‘yan tsiraru da mai shari’a Jane Esienanwan Inyang ta yanke ta amince da daukaka karar tare da umartar hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ta gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 90.
A wani labarin kuma, Yuletide: Hukumar FRSC ta Gargadi Fasinjoji Game da Tafiye-Tafiyen Cikin Dare
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta gargadi fasinjoji da su guji yin tafiye-tafiye cikin daddare a lokacin bukukuwan kirsimeti
“Mutane suna da ‘yancin yin tafiya, amma hukumar kiyaye hadurra, tana da hurumin daukar matakan da za su taimaka wajen rage hadurran hanyoyi
Da yawan lokuta “Idan wani hatsari ya faru, wani lokacin ba sa samun masu taimako ko kuma yana ɗaukar lokaci kafin a sami waɗanda za su taimaka,”
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta gargadi fasinjoji da su guji yin tafiye-tafiye cikin daddare a lokacin bukukuwan kirsimeti saboda illar da za su iya fuskanta.
Mista Ibrahim Maiyaki-Bazama, Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Katsina ne ya yi wannan gargadin yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Katsina.