- An shawarci gudanarwar hukumar JAMB da ta tsawaita ingancin sakamakon makinta sama da shekara guda domin masu neman gurbin shiga makarantar da ba a ba su damar yin amfani da irin wannan sakamako ba
- Mafi kyawun gadon da mutum zai bari ga matasa shi ne ilimi mai inganci kuma mai araha
- Abin da JAMB ke yi a yanzu shi ne karbar kudaden ‘yan Najeriya da kuma jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba dole ba
An shawarci Hukumar gudanarwar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB da ta tsawaita ingancin sakamakon makinta sama da shekara guda domin masu neman gurbin shiga makarantun da ba a ba su damar yin amfani da irin wannan sakamako ba wajen neman gurbin karatu a karo na gaba, Tribune Online ta rahoto.
Hakan dai zai “Iya kawar da matsalolin kudi daga ‘yan Najeriya.”
KARANTA WANNAN: Gobara ta Tashi a Ofishin Bankin Duniya
Wannan bukatar ta fito ne daga hannun kungiyar wayar da kan jama’a ta kungiyar malaman makarantu ta kasa (ASUP).
Shugaban Kungiyar Kwamared Abdullahi Yelwa a wata makala da ya gabatar a matsayin babban bako a taron ‘first Bauchi South Stakeholders Interactive Session’ wanda Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu Buba Umar ya shirya, wanda ya gudana a ranar Asabar a Event Center dake Bauchi.
Yalwa ya kuma bukaci Sanatan da ya bayar da tallafin kudi wanda zai kula da hazikan dalibai amma marasa galihu.
A cewarsa, mafi kyawun gadon da mutum zai bari ga matasa shi ne ilimi mai inganci kuma mai araha.
Yalwa ya bayyana cewa, abin da JAMB ke yi a bayyane yake na karbar kudaden ‘yan Najeriya da ke neman shiga manyan makarantun kasar nan.
Babban Malami na kwalejin fasaha ta Abubakar Tatari Ali (ATAP) ya yi mamakin dalilin da ya sa hukumar JAMB da ya kamata ta zama cibiyar gwamnati mai bin tsarin yi wa hidima ta koma bangaren samar da kudaden shiga ta yadda hakan ke jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba dole ba.
A cewarsa, “Akan shigar da dalibai zuwa manyan makarantu, musamman na lura da yadda hukumomin kula da harkokin ilimi, musamman JAMB a matsayinta na gwamnati, suka zama cibiyar samar da kudaden shiga maimakon cibiya mai dogaro da kai.
“Abin da JAMB ke yi a yanzu shi ne karbar kudaden ‘yan Najeriya da kuma jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba dole ba da kuma kulle guraben karatu a maimakon fadadawa da kara damar shiga manyan makarantu.
“Zabuka guda hudu da aka yaba a JAMB ko UMTE abin mamaki ne, domin a zahiri da kuma a aikace, zabin jami’oi ko kwalejojin Ilimi ko na fasaha daya ne kawai. Komai mene ne makin ku, idan ba za ku iya samun shiga a cikin zaman na yanzu ba, maki ɗinku ba shi da amfani, dole ne ku sake yin sa.
“Wannan yana mai da hankali ne kan samar da kudaden shiga da kuma wannan batu na canza jami’oi akai-akai domin duk wata makaranta da ba a zabinku na farko ba, ba za ta iya ba ku damar shiga ba. Don haka, babu buƙatar zaɓi na biyu, na uku ko na huɗu idan ba za ku iya samun shiga a can ba.
“Dole ne ku koma JAMB kuma ku biya kudade ku canza jami’a ko kwaleji. Don haka ya kamata JAMB ta daina yaudarar ‘yan Nijeriya, su daina barnatar da dukiyar ‘yan Nijeriya, mu mutunta wadannan zabuka.
“Idan ba za ku iya samun izinin shiga kowacce makaranta a zabi na farko ba, sauran su ba ku gurbin shiga don kada yaranmu su fuskanci wahala.”
A wani labarin kuma, Wata Mummunar Gobara ta Kone Dakunan Kwanan Dalibai
Kimanin dalibai 10 na Jami’ar Olabisi Onabanjo, Ago Iwoye, sun yi asarar dukiyoyinsu masu daraja sakamakon wata gobara da ta tashi a wani dakin kwanan dalibai
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan samun Wutar Lantarki Mai karfi
Gwamnatina za ta ci gaba da daukar matakan shawo kan matsalolin da jama’a ke ciki tare da ganin jin daɗin ɗalibai ya kasance mafi mahimmanci ga gwamnati
Kimanin dalibai 10 na Jami’ar Olabisi Onabanjo, Ago Iwoye, sun yi asarar dukiyoyinsu masu daraja da suka hada da tufafi, littafai da takardun shaida, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani dakin kwanan dalibai masu zaman kansu da ke titin Funmidara Cokers, Ijebu-Igbo a karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar Ogun.
An ce lamarin ya faru ne a makon jiya Talata saboda karuwar wutar lantarki