- Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa kimanin mayakan Boko Haram guda dubu 160,000 da iyalansu sun mika wuya
- Mika wuyan nasu ya samo asali ne sakamakon namijin kokarin da sojojin Najeriya suka yi akan su
- Gwamnan ya nemi goyon bayan sojoji ta fuskar bunkasa ma’aikata domin baiwa jihar damar dakile yaduwar kananan makamai
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa kimanin mayakan Boko Haram guda dubu 160,000 da iyalansu sun mika wuya.
A cewarsa, mika wuyan nasu ya samo asali ne sakamakon rashin kishin kasa da sojojin Najeriya suka yi akan su.
KARANTA WANNAN: Dalilin da Yasa Tinubu Ya Kamata Ya Sake Duba Nadin Mukamaan RECs – Tsohon Shugaban INEC Jega
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da ministan tsaro tare da hafsoshin tsaro suka kai ziyarar aiki zuwa rundunar, Operation Hadin Kai, OPHK, a Maiduguri.
Sai dai ya nemi goyon bayan sojoji ta fuskar bunkasa ma’aikata domin baiwa jihar damar dakile yaduwar kananan makamai da ke kan iyaka.
“Muna da tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar amma tsaro a yankin arewa maso gabas na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiyar kasar saboda tabarbarewar iyakokin da kasashen Nijar, Kamaru da Jamhuriyar Chadi.
“Dole ne mu tabbatar da cewa ba mu da mafakar ISWAP a arewa maso gabas saboda yanzu yankin Sahel ya zama babbar matsala,” in ji shi.
A wani labarin kuma, EPL: ‘Ka Dakatar da Yin Murna Kamar Ronaldo’ – Dan Wasa Vidal Ya Soki Garnacho
Tsohon dan wasan tsakiya na Chile Arturo Vidal ya soki Alejandro Garnacho na Manchester United da yin koyi da yadda Ronaldo keyin murna lokacin Daya zura kwallo
“Abin da ba daidai ba ne ko abin da ban fahimta ba, shi ne dalilin da ya sa yake murna kamar Cristiano”
Wannan dai na zuwa ne yayin da Dan wasan ya zura kwallo a raga inda ya barke da murna
Tsohon dan wasan tsakiya na Chile Arturo Vidal ya soki Alejandro Garnacho na Manchester United da yin koyi da yadda Cristiano Ronaldo keyin murna lokacin Daya zura kwallo.
Garnacho ne ya fara zura kwallo a ragar kungiyar ta Everton da bugun daga kai sai mai tsaron gida.