- Wata mata ‘yar kasar Uganda mai shekaru 70 ta haifi ‘ya’ya biyu, kamar yadda likitanta ya bayyana
- Tuni dai wannan dattijuwa ta bayyana farin cikinta da zuwan tagwayen da aka haifa a matsayin abin al’ajabi bayan ta shafe tsawon Shekaru Bata haihu ba
- Sai dai dattijuwar mahaifiyar tagwayen ta nuna rashin jin dadin yadda abokin zamanta bai ziyarce ta ba tun da ta zo asibiti domin haihuwa
Wata mata ‘yar kasar Uganda mai shekaru 70 ta haifi ‘ya’ya biyu, kamar yadda likitanta ya bayyana a ranar Alhamis, lamarin da mahaifiyar ta bayyana a matsayin abin al’ajabi.
Safina Namukwaya ta bayyana farin cikinta da zuwan tagwayen da aka haifa a ranar Laraba a wani asibitin Kampala babban birnin kasar, inda ta samu kulawar haihuwa.
KARANTA WANNAN: WAFCON 2024: Super Falcons ta Lallasa Cape Verde Da Ci 5-0
Doctor Edward Tamale Sali, wanda ya kula da juna biyu da haihuwa, ya shaida wa manema labarai cewa “Wannan wata babbar nasara ce, na haifar tagwaye ga babbar mahaifiyar Afirka tana da shekaru 70.”
Ya ce mahaifiyar da jariran – namiji da mace – har yanzu suna cikin kulawar asibitin mata na kasa da kasa da cibiyar haihuwa da ya kafa, amma suna cikin koshin lafiya.
“Babu yadda za a yi in bayyana farin cikina a halin yanzu,” in ji Namukwaya, wanda ke zaune a karkarar Masaka mai tazarar kilomita 120 (mil 75) dake yammacin Kampala.
“A shekaru 70 lokacin da aka dauke ni mai rauni, ba zan iya yin ciki da haihuwa ba, ko kula da jariri, kuma ga abin al’ajabi na tagwayen,” kamar yadda ta shaida wa AFP ta wayar tarho.
Namukwaya ta ce a baya ta haifi ‘ya mace a shekarar 2020, bayan da aka yi mata ba’a a matsayin “la’ananiya” wadda a baya ta kasa haihuwa.
Ta ce mijinta na farko ya rasu a shekarar 1992, inda ya bar ta ba tare da ‘ya’ya ba, kuma ta hadu da abokin zamanta a shekarar 1996.
Sai dai Namukwaya ta nuna rashin jin dadin yadda abokin zamanta bai ziyarce ta ba tun da ta zo asibiti domin haihuwa.
“Wataƙila bai ji daɗin haihuwar tagwaye ba saboda maza ba sa son sanin cewa kana ɗauke da yaro fiye da ɗaya a cikin mahaifa saboda fargabar yiwuwar nauyin da ke tattare da hakan.”
A wani labarin kuma, PDP ta Zargi Gwamna Alia da Karya Doka Bisa Nada kwamitocin Riko na Kananan Hukumomi
Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnan Benue Alia da tauye tsarin doka bisa nadin kwamitocin riko na kananan hukumomin jihar
PDP ta ce ayyukan Gwamnan sun sha bamban da alkawurran yakin neman zabensa a zaben 2023
A cewar PDP matakin ba shi da goyon bayan doka, kuma ya sanya ayar tambaya game da kudurin gwamnan na samar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi
Jam’iyyar PDP ta zargi gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwe da tauye tsarin doka bisa nadin kwamitocin riko na kananan hukumomin jihar a kwanakin baya.
Matakin a cewar jam’iyyar PDP, ba shi da goyon bayan doka, kuma ya sanya ayar tambaya game da kudurin gwamnan na samar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi da aka alkawarta.