- Makwanni kadan da fara gasar cin kofin Najeriya ta 2023-24, NNL, babban kocin kungiyar Mighty Jets Aminu Musa ya yi murabus
- Bayan yin murabus tuni dai aka maye gurbin Musa da Sabon koci
- Sabon Kocin zai fuskanci babban kalubale a gabansa
Makwanni kadan da fara gasar cin kofin Najeriya ta 2023-24, NNL, babban kocin kungiyar Mighty Jets Aminu Musa ya yi murabus daga mukaminsa.
Musa ya kawo dalilai na kashin kansa da suka sa ya yanke shawarar barin kungiyar ta Jos.
KARANTA WANNAN: WAFCON 2024: Super Falcons ta Lallasa Cape Verde Da Ci 5-0
Might Jets sun yi canjaras da ci 2-2 a wasanninsu na biyu na kakar wasa ta bana a karkashin kocin.
Tuni dai aka maye gurbin Musa da Najib Mabo.
Mabo zai fara aiki ne a kungiyar a karawar da za su yi da Nasarawa United a filin wasa na Lafia City ranar Asabar.
Mighty Jets ce ta shida a teburin rukunin C na taron Arewa.
A wani labarin kuma, Zaben 2024: Mataimakina Yana da Damar Tsayawa Gakara – Gwamna Obaseki Ya Magantu
Gwamnan Edo Godwin Obaseki ya bayyana cewa mataimakinsa Philip Shaibu yana da damar tsayawa takarar gwamna a 2024
Jam’iyyar PDP za ta yanke shawara ko Mataimakina zai kasance mai rike da tutar jam’iyyar a cewar Gwamna Obaseki
Duk da dambarwar data biyo baya Mataimakin Gwamna Obaseki aranar litinin ya bayyana a hukumance yana son tsayawa takarar gwamnan jihar
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayyana cewa mataimakinsa Philip Shaibu yana da damar tsayawa takarar gwamna a shekarar 2024.
Obaseki, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta yanke shawara ko Shaibu zai kasance mai rike da tutar jam’iyyar.