- Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakin rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers
- Jirgin ya yi hatsari ne jim kadan bayan ya tashi domin yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa
- Tuni shugaban hafsan sojin saman Air Marshal Hasan Abubakar ya nufi wurin da lanarin ya afku domin ganin halin da ake ciki
Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakin rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a ranar Juma’a a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Edward Gabkwet, kakakin NAF, ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Jam’iyyar APC ta Yi Kiran a Gaggauta Cafke Dan Takarar Gwamna Na SDP
Ya ce jirgin mai lamba NAF MI-35P ya yi hatsari ne da misalin karfe 7:45 na safe jim kadan bayan ya tashi domin yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a jihar Ribas.
Ya kara da cewa duk wanda ke cikin jirgin ya tsira sai dai kuma sun samu “Kananan raunuka”.
Gabkwet ya kara da cewa an kaisu cibiyar kula da lafiya ta NAF da ke Fatakwal.
Sanarwar ta kara da cewa, “A halin yanzu shugaban hafsan sojin saman Air Marshal Hasan Abubakar yana kan hanyarsa ta Fatakwal domin ganin halin da ake ciki, ya kuma duba lafiyar ma’aikatan tare da ba da umarni.”
A wani labarin kuma, Mutane Hudu Sun Rasa Rayukan Su Bisa Zargin Amfani da Maganin Kanjamau Na Gargajiya
Kungiyar masu fama da cutar kanjamau a Najeriya (NEPWHAN) a Gombe, ta bayyana cewa mambobinta hudu sun mutu bisa zargin amfani da maganin cutar HIV na gargajiya
Yawaitar amfani da maganin gargajiya don maganin cutar kanjamau a jihar ya zama abin damuwa saboda karuwar irin wadannan magunguna
Akwai bukatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su tsara tare da duba yadda ake yawo maganin gargajiya na cutar kanjamau a jihar
Kungiyar masu fama da cutar kanjamau a Najeriya (NEPWHAN) a jihar Gombe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa mambobinta hudu sun mutu bisa zargin amfani da maganin cutar kanjamau na gargajiya.
Jami’in tsare-tsare na kungiyar, Mista Muhammad Ibrahim ne ya bayyana haka a Gombe a wani taron tunawa da ranar cutar kanjamau ta duniya ta 2023.