- Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen ya amince cewa dan wasan baya na Real Madrid, Antonio Rudiger yana bata masa rai
- Dan wasan na Jamus ya hana dan wasan na Najeriya sakat yayin da Madrid ta doke Napoli
- Dan Wasa Rudiger ya yarda cewa Osimhen Yana da wuyar sha’ani
Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen ya amince cewa dan wasan baya na Real Madrid, Antonio Rudiger yana bata masa rai a duk lokacin da suka fuskanci juna.
Dan wasan na Jamus ya hana dan wasan na Najeriya sakat yayin da Madrid ta doke Napoli da ci 4-2 a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Sokoto ta Gabatar Kasafin Kudin 2024 na N270bn Ga Majalisa
Duk da haka, Rudiger ya yarda ta labarinsa na Instagram cewa Osimhen yana da wuyar karewa.
Da yake raba hoton kansa da Osimhen suna fafatawa a filin wasa, ya rubuta, “Ni Naija brother strong.”
Osimhen ya sake wallafa sakon Rudiger a cikin labarinsa na Instagram tare da taken; “Kowane lokaci ina yaƙi da kai. Barka da sake saduwa da ku Dan uwana.”
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: Kasafin Kudin 2024 Ya Tsallake Karatu Na Biyu
Majalisar wakilai ta amince da kasafin kudi na Naira tiriliyan N27.5tn na shekarar 2024 Wanda ya Tsallake Karatu na biyu
Kudurin kasafin kudin shekarar 2024 ya kasance a matsayin kasafin kudin da ya shafi al’umma da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya
‘Yan majalisar sun nemi a sake duba kasafin kudin da aka ware wa Wasu fannoni da Suka shafi ‘yan Najeriya
Majalisar wakilai ta amince da kasafin kudi na Naira tiriliyan N27.5tn na shekarar 2024 wanda ya tsallake Karatu na biyu a ranar Juma’a.
Da take jagorantar muhawarar kan ka’idojin kasafin, mamba mai wakiltar mazabar Kosofe ta Jihar Legas, Kafilat Ogbara, ta bayyana kudurin kasafin kudin shekarar 2024 a matsayin kasafin kudin da ya shafi al’umma da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.