- Gwamnatin Tarayya ta raba Naira biliyan 135.4 ga Jihohi da Babban Birnin Tarayya, biyo bayan tantance sakamako shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya na COVID-19
- An fitar da kudaden ne bisa sakamakon da jihohi da babban birnin tarayya Abuja suka samu a kokarinsu na tallafawa talakawa da marasa galihu
- Shirin na da nufin rage radadin tattalin arziki ga talakawa da marasa galihu ke fuskanta a Najeriya sakamakon kulle a lokacin rikicin COVID-19
Gwamnatin Tarayya ta raba Naira biliyan 135.4 ga Jihohi da Babban Birnin Tarayya, biyo bayan tantance sakamako mai zaman kansa na biyu da aka samu a karkashin shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya na COVID-19 a wani mataki na magance talauci mai dimbin yawa da tallafawa marasa galihu a Najeriya, Punch ta rahoto.
https://punchng.com/covid-19-fg-releases-n135-4bn-to-states-fct/?amp
Ko’odinetan shirin NG-CARES na kasa Abdulkarim Obaje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in yada labarai da sadarwa na NG-CARES Suleiman Odapu ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2024 Ga Majalisar Dokokin Jihar
Shirin NG-CARES wani aiki ne na tallafin Bankin Duniya-Jihohi wanda aka aiwatar a duk jihohi 36 da FCT.
Shirin na da nufin rage radadin tattalin arziki da zamantakewa da talakawa da marasa galihu ke fuskanta a Najeriya sakamakon kullen da aka yi a lokacin rikicin COVID-19.
An tsara aikin a matsayin Shiri na Sakamako, biyan jihohi da kuma FCT don abubuwan da suka kashe idan sun aiwatar da aikin kamar yadda aka tsara a cikin Yarjejeniyar Kudade, Manufar Sakar Kudade, da Yarjejeniyar Wakilin Tabbatarwa mai zaman kanta.
Obaje ya ce an fitar da kudaden ne bisa sakamakon da jihohi da babban birnin tarayya Abuja suka samu a kokarinsu na tallafawa talakawa da marasa galihu a Najeriya karkashin shirin NG-CARES da kuma magance talauci mai dimbin yawa a kasar.
Sanarwar ta kara da cewa “jihohi uku da suka fi iya aiki a wannan zagaye na biyu na tantancewa sune Nasarawa da ta samu Biliyan N13,697,828,496.96, sai Cross River Naira biliyan N10,944,747,818.84 da kuma Zamfara Mai Naira biliyan N10,231,055,267.82.”
Obaje ya kuma yabawa Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, bisa goyon bayan da yake bayarwa wajen gudanar da shirin NG-CARES a fadin kasar nan.
Ya kuma yabawa Gwamnonin Jihohi da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja da Bankin Duniya bisa bayar da tallafi.
A wani labarin kuma, An Ceto Wata Jaririya Sabuwar Haihuwa da Aka Yi Watsi da Ita
Yanzu haka dai an ceto wata jaririya ‘yar kwana daya da aka yi watsi da ita a jihar Neja
An nannade jaririyar da fata kuma aka bar ta babu tufafi
Abin tausayi, kafin dauke jaririyar daga wurin da aka yasar da ita har Wasu kwarika sun fara mamaye ta
Yanzu haka dai an ceto wata jaririyar ‘yar kwana daya da aka yi watsi da ita a unguwar Tayi da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
A cewar wata majiya, an gano jaririyar ne sa’o’i kadan bayan wata wanda ba a san ko wacece ba ta yasar da ita a yammacin ranar Asabar.