- Jam’iyyar APC ta kaddamar da kwamitin mutane 11 da zai duba sakamakon zaben gwamnan Kogi da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba
- Sharuddan kwamitin shi ne tantance duk wani lamari da ‘ya’yan jam’iyyar ke aikatawa tare da bayar da shawarar da ta dace kan ayyukan ladabtarwa
- Taron ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar APC da manyan jami’ian Gwamnatin Jihar
Jam’iyyar APC ta kaddamar da kwamitin mutum 11 da zai duba sakamakon zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, Daily Post ta rahoto.
Da yake jawabi yayin kaddamar da taron a sakatariyar jam’iyyar da ke Lokoja a ranar Talata, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kogi, Abdullahi Bello, ya ce daya daga cikin sharuddan kwamitin shi ne tantance duk wani lamari da ‘ya’yan jam’iyyar ke aikatawa tare da bayar da shawarar da ta dace kan ayyukan ladabtarwa.
KARANTA WANNAN: Mataimakiyar Gwamnan Kaduna ta Jagoranci Tawaga Don Jajantawa Wadanda Harin Bam Ya Shafa
Bello ya ci gaba da cewa, kwamitin zai kuma yi nazari tare da bayyana irin rawar da ‘ya’yan jam’iyyar suka taka wajen gudanar da zaben kafin da lokacin da kuma bayan gudanar da zaben.
A cewarsa, ana sa ran kwamitin zai gudanar da nazari dalla-dalla kan yadda aka gudanar da zaben a kowace karamar hukuma ta jihar.
Bello ya kara da cewa, ya kamata kwamitin ya yi kokarin zakulo ‘yan jam’iyyar da suka nuna ayyukan biyayya, jajircewa wajen tunkarar yanayi na siyasa a lokacin zabe tare da ba su shawarar samun isashen karramawa da kuma lada.
“Duk da cewa zabe ya zo ya wuce, illar da ta samu da faduwa har yanzu suna tare da mu, gaskiya ne a yayin da muka taka rawar gani a kananan hukumomi da dama, sakamakonmu a wasu da dama ya gaza tsammani.
“A wannan karon, muna da burin sanin abin da ya faru a kowacce karamar hukumar 21 da ta gabata, da lokacin da kuma bayan gudanar da zaben ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023,” in ji Bello.
Mambobin kwamitin sun hada da kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Hon. Aliyu Umar Yusuf (Shugaba), Farfesa Usman Ogbo, (Sakatare), Hon. Funsho Olumoko, Barista James Fabola, Sanata Atai Aidoko, Hon. Yakubu Okala, Hon. Idris Ozi Shaib, Hon. Abdulsalami Ibrahim Ahovi, Barista Ladi Jatto, Alh. Hadi Ametuo, da kuma Hon. Abubakar Bashir Gegu.
A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Neja Ta Bukaci Gwamnatin Jihar ta Tallafawa Wadanda Gobara ta Shafa
Majalisar dokokin Neja ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta baiwa hukumar NSEMA ta jihar Neja umarnin taimakawa wadanda gobara ta rutsa da su
Majalisar ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa cibiyoyin kashe gobara a Karamar hukumar da ma sauran kananan hukumomin jihar
“Ya kamata gwamnatin jihar ta gyara wasu sassan titunan da suka gaza a Karamar hukumar, saboda rashin kyawun titin ne ya hana jami’an kashe gobara su mayar da martani kan lokaci.”
Majalisar dokokin jihar Neja ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta baiwa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja umarnin taimakawa wadanda gobara ta rutsa da su a karamar hukumar Paiko da ke jihar.
Haka kuma ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa cibiyoyin kashe gobara a Karamar hukumar da ma sauran kananan hukumomin da ba su da irin wadannan kayayyakin.