- Dan wasan kwallon kafa mai suna Sodiq Adebisi dan asalin jihar Ogun ya rasu bayan ya fadi yayin atisaye a filin wasa
- Lokacin da abokan wasansa suka ga matashin ya fadi, tuni suka garzaya da shi asibitin jiha
- Iyalin Marigayin sun ce ba sa son wani bincike kuma suna son a binne marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
Dan wasan kwallon kafa mai suna Sodiq Adebisi dan asalin jihar Ogun ya rasu ne bayan da ya fadi yayin atisaye a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.
Rahotanni sun ce dan wasan yana atisaye da wasu ‘yan wasan kwallon kafa a ranar Asabar lokacin da lamarin ya faru.
KARANTA WANNAN: Wata Sabuwa: Majinyaciya ta Arce Daga Asibiti Saboda Gaza Biyan Kudin Magani
Lokacin da abokan wasansa suka ga matashin mai shekaru 34 a duniya ya fadi, sai suka garzaya da shi asibitin jihar da ke Ijebu-Ode.
Sai dai duk da irin jarumtakar da kwararrun likitocin asibitin suka yi, an tabbatar da rasuwarsa a ranar da aka kai shi asibiti.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, a ranar Talata ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa, dan’uwan marigayin, Ganiyu Adebisi, ya garzaya ofishin ‘yan sanda na Igbeba domin neman a binne gawar.
“Dan’uwansa ya zo ne ya kai rahoton faruwar lamarin a sashen mu na Igbeba. Iyalin sun ce ba sa son wani bincike kuma suna son a binne marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,”in ji Odutola.
A wani labarin kuma, PDP ta Bada Umarnin Janye Duk Wasu Kararrakin Jam’iyyar da Ke Gaban Kotuna
Jam’iyyar PDP ta umurci duk masu shigar da kara a cikin jam’iyyar da su janye karar da suka shigar a kotu
PDP ta bayyana cewa kwamitin ya bada umarnin ne bayan tayi nazari sosai kan halin da jam’iyyar ke ciki
NWC ya bukaci dukkan shugabannin jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da kuma ‘ya’yan jam’iyya da su ci gaba da kasancewa da hadin kai
Jam’iyyar PDP a Ranar Talata a Abuja ta umurci duk masu shigar da kara a cikin jam’iyyar da su janye karar da suka shigar a kotu.
Jam’iyyar ta bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Mista Debo Ologunagba ya fitar bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar NWC karo na 578.