- Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar reshen jihar Imo, Charles Ugwu
- An dakatar da Shugaban jam’iyyar ne bisa zarginsa da aikata wasu laifuka
- Dakatarwar ba ta da wani tasiri kuma ba ta yi daidai da ka’idoji da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ba
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa, a ranar Alhamis, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar reshen jihar Imo, Charles Ugwu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa an dakatar da Ugwu, tsohon ministan kasuwanci da masana’antu ne a ranar Talata bisa zarginsa da aikata ba daidai ba da kuma rashin biyayya.
KARANTA WANNAN: Kotu Ta Kori Kwamitin Riko Na PDP, ta Mayar da Tsoffin Shugabannin Jam’iyyar
Don haka ne aka nada Chidi Dike shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar karamar hukumar Okigwe a matsayin shugaban riko na jam’iyyar a jihar Imo, Punch ta rahoto.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa, NWC, a taronta na 579, ta bayyana dakatarwar Ugwu a matsayin ba komai ba.
Ologunagba ya bayyana cewa dakatarwar ba ta da wani tasiri kuma ba ta yi daidai da ka’idoji da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ba (kamar yadda aka gyara a shekarar 2017).
Sanarwar ta kara da cewa, “Don haka hukumar NWC ta bukaci dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki, mambobin kungiyar, da jiga-jigan magoya bayan jam’iyyar mu a jihar Imo da su yi musu jagora.
“NWC ya umurci dukkan ’ya’yan jam’iyyar a jihar Imo da su ci gaba da kasancewa tare kuma su ci gaba da yin aiki tare domin moriyar jam’iyyarmu baki daya.”
A wani labarin kuma, Adamawa: Fintiri Ya Dora Laifin Rashin Tsaro a Kan Iyakokin Kasa da Kasa da Suka Lalace
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce lallacewar iyakokin kasa da kasa ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a jihar
Ya Kamata NIS ta Samar da fasahar zamani domin tabbatar da tsaron iyakokin kasa da kasa da ke kewayen jihar Adamawa domin dakile kalubalen tsaron da ake fuskanta
Mafi yawan abubuwan da ke haifar da tabarbarewar tsaro suna fitowa ne daga kan iyakokin da ba su da kyau saboda yawancin masu aikata laifukan da ke aiki a jihar baki ne
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce lallacewar iyakokin kasa da kasa ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar sabon shugaban hukumar shige da fice ta kasa NIS Mohammed Adamu, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ranar Alhamis.