- Yayin da Najeriya ke fama da karancin kudi, babban bankin Najeriya ya gargadi ‘yan Najeriya game da yada jabun takardun kudin Naira
- Tuni CBN ya ba da tabbacin cewa yana aiki da jami’an tsaro domin kamo masu laifin
- Duk wanda aka Kama da aikata laifin zai Fuskanci hukuncin zaman gidan yari na shekaru 5
Yayin da Najeriya ke fama da karancin kudi, babban bankin Najeriya ya gargadi ‘yan Najeriya game da yada jabun takardun kudin Naira.
A ranar Juma’a ne babban bankin ya bayar da wannan gargadin a cikin wata sanarwa mai taken ‘Hattara da jabun takardun kudin Naira da ke kewayawa Cikin al’umma’.
KARANTA WANNAN: Gombe: Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Gabatar da Tallafin Kudi N80m Ga Iyalan Jami’an da Suka Rasu
Bankin ya bukaci dukkan bankunan ajiya na kudi, gidajen kudi, ofishin canji da sauran jama’a da su kara taka tsantsan tare da daukar duk matakan da suka dace.
A Cikin sanarwar CBN “Ya ba da tabbacin cewa yana aiki da jami’an tsaro domin kamo masu laifin.
“An jawo hankalin Babban Bankin Najeriya (CBN) kan yadda wasu daidaikun mutane ke yawo da jabun takardun kudi, musamman manyan jami’o’i domin yin mu’amala a kasuwannin abinci da sauran cibiyoyin kasuwanci a manyan biranen kasar nan.
“Don kauce wa shakku, sashe na 20 (4) na dokar CBN shekarar 2007 da aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana cewa: “Zai zama laifin da za a yanke hukuncin zaman gidan yari na kasa da shekaru 5 ga kowane mutum ya yi karya, ya aikata, ko kuma ya yi jabun duk wata takardar kudi ko tsabar kudi da Bankin ya fitar wanda ya halatta a Najeriya.”
“CBN na ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro da abin da ya dace domin karbe takardun kudin Naira na bogi, kamawa da hukunta masu yin jabun kudaden, haka kuma ana kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargi yana da jabun naira ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ko kuma reshe na hukumar Babban Bankin Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa “A halin da ake ciki, dukkanin bankunan ajiya na kudi, gidajen kudi da ofishin canji da sauran jama’a an umurce su da su kara taka tsantsan tare da daukar duk matakan da suka dace don dakile karbuwa da rarraba kudaden jabun kudaden”, in ji sanarwar.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa barazanar karancin Kudin Naira ta kara ta’azzara a wasu sassan Abuja yayin da ATM suka kasa rarraba kudi a babban birnin kasar.
A wani labarin kuma, Kogi: Masu Kiwon Dabbobi 39k Za su Ci Gajiyar Dala Miliyan 500 Daga Bankin Duniya
Masu kiwon dabbobi 39,000 a jihar Kogi nan ba da jimawa ba za su ci gajiyar tallafin kudi dala miliyan 500 na bankin duniya
Aikin na da nufin inganta kiwon dabbobi ta hanyar kasuwanci da sayarwa don bunkasa riba ga manoman kasar nan
“Za a samar da ciyawa ta yadda dabbobi za su samu isasshen abinci ta yadda za a rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya
Masu kiwon dabbobi 39,000 a jihar Kogi nan ba da jimawa ba za su ci gajiyar tallafin kudi dala miliyan 500 na bankin duniya da nufin karfafawa manoman dabbobi a fadin kasar nan.
Aikin wanda aka fara shi gaba daya, ana sa ran zai kama mutane 30,000 da za su ci gajiyar shirin kai tsaye da mata 9,000 a jihar.