- Masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur na Downstream sun tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an samu raguwar farashin man fetur sosai
- Masu Ruwa da tsakin sun danganta hauhawar farashin man da ake samu a halin yanzu da shigo da shi daga kasashen waje
- Akwai tabbacin kashi 100 cikin 100 na farashin man fetur zai ragu yayin da matatun man suka sake fara aiki
Masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur na Downstream sun tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an samu raguwar farashin man fetur sosai, lamarin da ke nuni da cewa nan ba da dadewa ba za a shawo kan tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a bangaren makamashi, Daily Post ta rahoto.
Suna hasashen faduwar farashin man fetur musamman a matatar man Fatakwal da ke jihar Ribas a watan Janairu.
KARANTA WANNAN: Gwamna Otti Ya Gabatar Da Kasafin Kudi na Naira N567bn Ga Majalisar Dokokin Abia
Kenneth Korie, Shugaba na Kasa kuma shugaban kwamitin amintattu na NOGASA, tare da Dr. Billy Harry, takwaransa na PETROAN, sun bayar da wannan tabbacin daban bayan kaddamar da sassan jihar Akwa Ibom na hukumomin kula da masana’antu guda biyu a Ibom Icon Hotel a Uyo, Jihar Akwa Ibom, ranar Talata.
Da suke bayyana kwarin gwiwa, sun bayyana cewa suna da tabbacin kashi 100 cikin 100 na farashin man fetur zai ragu yayin da matatun man suka sake fara aiki a watan Janairu.
Korie ya danganta hauhawar farashin man da ake samu a halin yanzu da shigo da shi daga kasashen waje sannan ya kara da cewa gyara da inganta matatun man da ke Fatakwal, Kaduna da Warri na da matukar muhimmanci wajen rage farashin kayayyakin.
“Eh, tabbas akwai fata, GMD NNPC ya ba da tabbacin hakan a gaban Majalisar Dokoki ta kasa. A duk tattaunawar da na yi, na yi ta tursasa matatar man Fatakwal domin ta shigo yanar gizo,” in ji Korie.
“Na tabbata Kashi 100% za a samu raguwar farashin man fetur da zarar matatunmu guda hudu da suka hada da matatar man Dangote suka fara Aiki, Amma bai kamata mu yi tsammanin farashin zai sauko kamar da ba, saboda tsadar canji, amma zai dan ragu da yadda yake a yanzu.”
A wani labarin kuma, Sakataren Gwamnatin Tarayya Akume Ya Nesanta Kansa Daga Daukar Ma’aikata Na Bogi
Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, ya nesanta kansa daga nade-naden mukamai na bogi da ake amfani da su wajen damfarar ‘yan Najeriya
An shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan da masu aikata wannan mugunyar dabi’a da ‘yan kungiyarsu tare da yin watsi da irin wadannan bayanan da ake yi
Tuni Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya Gargadi Masu kulla wannan makirci da su dai ko kuma su Fuskanci fushin doka
George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, ya nesanta kansa daga nade-naden mukamai na bogi da ake amfani da su wajen damfarar ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.
Sakataren ya yi watsi da bayanan karya da ke yawo a shafukan sada zumunta da kuma ta hanyar imel, saƙonnin kartakwana, da sauran tashoshi suna kira ga jama’a da su gabatar da takardun karatunsu don biyan kuɗi zuwa teburin da babu shi a ofishin sakataren gwamnatin tarayya da za a yi la’akari da nade-naden gwamnatin tarayya daban-daban.