- Majalisar dokokin Rivers, ta bayyana kujerun mambobin majalisar 27 da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC a matsayin wadanda Babu kowa
- Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ya barke tsakanin Gwamna mai ci Sim Fubara da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike
- Shugaban majalisar ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gudanar da sabon zabe cikin wa’adin da doka ta tanada
Majalisar dokokin jihar Rivers, a ranar Laraba, ta bayyana kujerun mambobin majalisar 27 da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC a jihar a matsayin wadanda Babu kowa.
Idan dai ba a manta ba, JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito a ranar Litinin din da ta gabata cewa ‘yan majalisa 27 da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai mulki zuwa APC a jihar.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gwamna Ribas Fubara Ya gabatar da kasafin Kudin 2024 ga Majalisar Dokoki Jihar
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ya barke tsakanin Gwamna mai ci Sim Fubara da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike.
Sai dai majalisar mai wakilai hudu karkashin jagorancin kakakin bangaren Edison Ehie, masu biyayya ga gwamnan jihar a ranar Laraba, ta ce matakin bayyana kujerun da babu kowa a kansu ya yi daidai da sashe na 109 (1) (g) da na 2 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya shekarar 1999 kamar yadda aka gyara.
Shugaban majalisar wanda ya karanta sunayen ‘yan majalisar da abin ya shafa, ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gudanar da sabon zabe cikin wa’adin da doka ta tanada.
“Masu girma abokan aiki, majalisar za ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta cike guraben ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da kuma gudanar da sabon zabe domin cike guraben da ke sama,” Ehie ya bayyana.
A wani labarin kuma, Kano: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Cafke Darakta da Wasu Mutane Biyu Bisa Zargin Zamba
Yanzu haka dai an yi ram da wani Darakta a ma’aikatar gwamnatin jihar Kano Abubakar Gambo da wasu mutane biyu bisa zargin zamba
Daraktan da mutanen boyi ana zargin su da karkatar da miliyoyin Naira ta hanyar yin gwanjon kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba
Tuni dai wadanda ake Zargin idon su ya raina fata ya yin da Suka fada komar ‘yan sanda
Yanzu haka dai an damke wani Darakta a ma’aikatar gwamnatin jihar Kano Abubakar Gambo da wasu mutane biyu tare da tsare su a sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar bisa zargin zamba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya tabbatar wa manema labarai kamun a ranar Talata.