- Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Dakta Musa Aliyu a matsayin kwararren shugaban hukumar ICPC bayan majalisar dattawa ta tabbatar da shi
- A ranar 16 ga watan Oktoba, 2023, Tinubu ya nada shugaban hukumar tare da sakataren Hukumar ta ICPC
- Sabon shugaban Hukumar ta ICPC Kafin nada shi ya rike mukamin Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Jigawa
Shugaban kasa Bola Tinubu a Ranar Laraba ya rantsar da Dakta Musa Aliyu a matsayin kwararren shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaka bayan majalisar dattawa ta tabbatar da shi.
Aliyu ya yi rantsuwar ne da misalin karfe 12:24 na rana a zauren majalisar zartarwa ta tarayya da ke Abuja.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Sanwo-Olu Ya Isa Majalisar Dokokin Legas Domin Gabatar da Kasafin kudin 2024
A ranar 16 ga watan Oktoba, 2023, Tinubu ya nada Aliyu tare da Mista Clifford Oparaodu a matsayin (Sakataren Hukumar ta ICPC).
Yayin da ofishin shugaban ya bukaci majalisar dattawan Najeriya ta amince da shi, sai dai mukamin sakataren hukumar ba haka yake ba.
“Saboda haka, nadin Mista Oparaodu a matsayin sakataren hukumar ya fara aiki nan take,” in ji mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jam’a, Ajuri Ngelale.
Aliyu wanda ya rike mukamin Babban Lauyan Jihar Jigawa tun a watan Satumbanr shekarar 2019 ya samu digirin digirgir, na biyu, da kuma digiri na uku a fannin shari’a.
An kuma nada shi a matsayin Babban Lauyan Najeriya wanda aka zaba a watan Oktoba 2023.
Shugaban ya kuma rantsar da shugaban hukumar da’ar ma’aikata ta tarayya, Farfesa Tunji Olaopa.
Olaopa ya yi rantsuwar ne da karfe 12:30 na rana bayan haka kuma wasu mambobin Hukumar 11 suka bi sahun.
Sun hada da wakilan Adamawa, Gombe, da Taraba, Dokta Daudu Jalo sai kuma Obong Eyoma (Akwa Ibom da Cross River), Dokta Chamberlain Nwele (Anambra, Ebonyi, da Enugu), Rufus Godwins (Rivers, Delta da Bayelsa), Dr. Adamu Hussein ( Neja da FCT) da Aminu Nabegu (Jigawa da Kano).
Sauran sun hada da Hindatu Abdullahi (Kaduna da Katsina), Shehu Aliyu (Kebbi, Sokoto, da Zamfara), Odekunle Aduke (Kogi da Kwara), Sarah Sosan (Lagos da Ogun) da Dr. Festus Oyebade (Osun da Oyo).
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Wata Sabuwa, Gwamnatin Ribas ta fara Ruguje Ginin Majalisar Dokokin Jihar
Rikicin siyasar Ribas ya dauki sabon salo a yayin da gwamnatin jihar ta fara rusa ginin majalisar dokokin jihar
Rusau din ya biyo bayan Zaman farko da ‘yan Majalisa Masu biyayya da Gwamnan Jihar Suka Yi
Majalisar dai ta Rasa kaso Mai tsoka na Mambobinta inda Suka sauya sheka zuwa jam’iyyar a dawa
Rikicin siyasar jihar Ribas ya dauki sabon salo a safiyar yau Laraba yayin da gwamnatin jihar ta fara rusa majalisar dokokin jihar.
Jaridar TRIBUNE ONLINE ta tattaro cewa kimanin Motocin rusau 10 ne suka shiga harabar majalisar a daidai lokacin da wasu ‘yan majalisar masu biyayya ga gwamnan jihar, Sim Fubara suka yi zaman farko.