- Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta haramta sayar da kayan wasan wuta, Naka Awut da sauran fasahohin zamani a jihar
- Yin amfani da kayayyakin wasan wuta na iya haifar da tashin hankali, wanda ke haifar da damuwa, tsoro da kuma rushewar zaman lafiyar jama’a
- Ana gargadi da kakkausar murya cewa duk dillali ko mazaunin jihar da ya kasa bin dokar, idan aka kama shi zai fuskantar fushin doka
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta haramta sayar da kayan wasan wuta, Naka Awut da sauran fasahohin zamani a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Abass ya yi gargadin cewa an dauki matakin ne saboda yana barazana ga tsaron jihar don haka a kauce masa.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa Suna Ganawar Sirri, Sun yi Allah-Wadai da Harin Bam a Kaduna
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Bright Edafe, ya fitar ranar Juma’a, inda aka rabawa manema labarai kwafin a garin Warri.
“Kwamishinan ‘yan sanda Wale Abass ya yi gargadin cewa yin amfani da kayayyakin wasan wuta na iya haifar da tashin hankali, wanda ke haifar da damuwa mara kyau, tsoro da kuma rushewar zaman lafiyar jama’a,” in ji sanarwar.
Ya ci gaba da cewa, “Bugu da kari, (kwamishinan’yan sanda) ya yi gargadi game da illar da ke tattare da amfani da shi, tare da lura da cewa zai iya ba da damar karkatar da mutane da ka iya ba masu laifi damar ci gaba da laifukansu da kuma jefa mazauna Jihar cikin hatsari.
“Kwamishinan ya yi gargadi da kakkausar murya cewa duk dillali ko mazaunin jihar da ya kasa bin dokar, idan aka kama shi, za a sanya shi fuskantar fushin doka.
“A kan wannan bayanin, an yi kira ga iyaye da masu kula da su da su sanya ido a kan unguwannin su tare da dakile amfani da kayayyakin wasan wuta a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
“CP Wale Abass ya bukaci mutanen Delta nagari da su kasance masu taka-tsan-tsan da kuma lura da tsaro yayin da yake jaddada kudirin rundunar da kuma shirye-shiryen kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin a lokacin Yulitide da kuma bayan haka.
“Kwamishanan ‘yan sanda a madadin jami’ai da ‘yan sanda, yana yiwa mutanen jihar Delta fatan alheri da bikin Kirsimeti da sabuwar shekara ba tare da laifi ba.”
A wani labarin kuma, Karin Wasu Kwamishinonin Uku Sunyi Watsi da Tafiyar Gwamnatin Fubara
A yanzu haka al’amura na cigaba da tabarbarewa wanda aka Kara samun ficewar Wasu Kwamishinonin uku daga majalisar zartarwa ta jihar Ribas
Murabus din nasu ya biyo bayan rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar tun bayan harin bam da aka kai a majalisar dokokin jihar
Shugaban Kwamitin Riko na APC a Jihar ya ce a karshen makon nan ne aka shirya kaddamar da sabuwar jam’iyyar APC, inda ya ce, “Za ku ga tsunami da zai faru haka nan da rana Tsaka
A yanzu haka al’amura na cigaba da tabarbarewa a Ranar juma’a wanda aka Kara samun ficewar Wasu Kwamishinonin uku daga majalisar zartarwa ta jihar Ribas.
Wadanda Suka Yi Watsi da Tafiyar Gwamnan Jihar su ne Kwamishinan Sufuri Dokta Jacobson Nbina; Kwamishinan Gidaje, Dokta Gift Worlu; da Kwamishinan Muhalli, Austen Ben-Chioma.