- Hukumar NDLEA, ta ce jami’anta sun kame wasu mutane biyu dauke da tabar wiwi kilogiram 171 a jihar Borno
- Kamen na daga cikin nasarorin da NDLEA ta samu a yakin da ake yi da miyagun kwayoyi a kasar
- Shugaban hukumar ta NDLEA ya bukaci Jami’an hukumar da su kara kaimi wajen yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a daidai lokacin da kakar Kirsimeti ke gabatowa
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce jami’anta sun kame wasu mutane biyu dauke da tabar wiwi kilogiram 171 a Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno.
Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Femi Babafemi shine wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN: Dole Ne Gwamnatin Tarayya da Jihohi Su Magance Talauci, Inji Tsohon gwamnan Kano
Baba Femi ya kuma lura da cewa kamen na daga cikin nasarorin da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta sake yin alkawari a yakin da ake yi da miyagun kwayoyi a kasar.
A ranar Talatar da ta gabata ne jami’an rundunar na jihar Borno da ke kan hanyar zuwa Maiduguri suka damke wadanda ake zargin, Bukar Ali mai shekaru 29 da Abacha Alhaji Fantami mai shekaru 20.
A jihar Borno, jami’an NDLEA a ranar Talata 12 ga watan Disamba sun kama Bukar Ali mai shekaru 29 da Abacha Alhaji Fantami mai shekaru 20 dauke da tabar wiwi kilogiram 171 a garin Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga.
“Sannan mutane uku da ake zargin Jamilu Haruna dan shekara 22 da Mohammed Hassan mai shekaru 23 da kuma Aminu Umar mai shekaru 50 an Kama su da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 57 a ranar Laraba 13 ga watan Disamba a shingen bincike na Tsafe, jihar Zamfara, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Zurumi, wani kauye da aka fi sani da ‘yan fashi,” in ji kakakin.
A cewar Babafemi, yayin da yake yaba wa jami’an hukumar da kame Masu laifin a fadin kasar nan cikin makon da ake nazari, shugaban hukumar ta NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya bukace su da su kara kaimi wajen yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a daidai lokacin da kakar yuletide ke gabatowa.
Shugaban hukumar ya ce ya kamata su tabbatar da daidaito daidai gwargwado da kokarin da suke na rage bukatun muggan kwayoyi
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: NCDC ta Tabbatar da Barkewar Cutar Zazzabin Dengue a Jihar Sokoto
Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Dengue a jihar Sokoto
NCDC tace an samar da tsarin mayar da martani mai inganci tare da samar da karfin sarrafawa don takaita hadarin yaduwarta zuwa wasu jihohi
Yawancin wadanda ake zargin suna kamuwa da cutar suna tsakanin shekaru 21-40
Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Dengue a jihar Sokoto a ranar Asabar.
Hukumar NCDC, a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce an gano bullar cutar ne a watan Nuwamban shekarar 2023.