- Hukumar NDLEA, ta cafke tan 7,590 na haramtattun kwayoyi da wasu abubuwa da suka kai sama da Naira biliyan 800
- A kokarin Yaƙi da Muggan Kwayoyi Hukumar tayi ram da mutane 42,105 masu safarar
- Haramtattun kwayoyi suna da alaka da aikata laifuka, musamman ta’addanci
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta cafke tan 7,590 na haramtattun kwayoyi da wasu abubuwa da suka kai sama da Naira biliyan 800 tare da kama masu safarar miyagun kwayoyi 42,105 cikin shekaru uku a fadin kasar nan.
Shugaban hukumar NDLEA Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ne ya bayyana haka a lokacin da babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ziyarci hedikwatar hukumar ta NDLEA a ranar Litinin a Abuja.
KARANTA WANNAN: Kirsimeti: Hukumar FRSC Za ta Tura Jami’anta 1,225 a Osun
Marwa ya ce haramtattun kwayoyi suna da alaka da aikata laifuka, musamman ta’addanci, garkuwa da mutane, da kuma tada kayar baya.
Ya kara da cewa “Dukkan su sun dogara ne da kwayoyi kafin su aiwatar da munanan ayyukansu, wannan ne ya sa NDLEA ta yi taurin kai tare da hana masu aikata miyagun laifuka damar yin amfani da miyagun kwayoyi.”
A cewarsa, hukumar ta NDLEA ta kuma lalata gonakin tabar wiwi mai hekta 1,057 a cikin wannan lokaci tare da samun nasarar hukunta masu laifi guda 8,350.
Ya kuma kara da cewa mutane 29,400 masu shaye-shayen kwayoyi ne aka basu shawarwari tare da gyara su a cikin lokaci guda.
“A cikin kimanin shekaru uku, mun kama masu safarar miyagun kwayoyi guda 42,105, ciki har da baron guda 46, mun kama wasu kwayoyin da bai wuce tan 7, 590 ba, kuma wannan ya kai kusan Naira biliyan 800,” in ji Marwa ga Janar Musa.
Ya yabawa rundunar sojin kasar bisa jajircewa, biyayya, sadaukarwa da jajircewa wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya a kasa da irin tallafin da ake baiwa hukumar ta NDLEA.
Ya ce hakan ya kasance a fannin makamai da alburusai da horar da jami’ai da maza na hukumar.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kogi Ta Damke Masu Hakar Ma’adanai 10 Ba Bisa Ka’ida Ba
Gwamnatin Kogi ta kama wasu masu hakar ma’adinai 10 da suke gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba
Duk masu hakar ma’adinai a jihar Kogi dole ne su yi aiki bisa tsarin doka
Gwamnatin jihar Kogi ta kama wasu masu hakar ma’adinai 10 da suke gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Ankpa.
Kwamishinan ma’adanai da albarkatun kasa na jihar Kogi, Bashiru Gegu, ne ya bayyana hakan a yammacin ranar Litinin a Ankpa lokacin da ma’aikatarsa tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta musamman kan safarar bindigogi da sauran laifuffuka ba bisa ka’ida ba, suka fara aiwatar da aikin Umarnin Gwamna Yahaya Bello na hana hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.