- Gwamnan Ribas Sim Fubara da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike hava, sun amince da kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar
- Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Kasa Tinubu ya gada Gwamnan da Wanda ya gada
- Kafin yanzu Rikicin Siyasar Rivers ya dauki Sabon Salo Daga bangarorin biyu
Gwamna Sim Fubara na jihar Ribas da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike hava, sun amince da kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Rikicin Ribas, Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Gwamna Fubara A Villa
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa an cimma wannan matsayar ne bayan da shugaba Bola Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki suka gana da bangarorin da ke rikici da juna a ranar Litinin.
A wani labarin kuma,Juyin Mulkin Soja Na Iya Yaduwa a Afirka – Minista
Ministan Harkokin Kasashen Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi gargadi game da bayyana sauyin gwamnatin da aka yi a yammacin Afirka
Idan ba a magance juyin mulkin ba zai iya mamaye daukacin nahiyar Afirka tare da kara kalubalantar ta’addanci da sauran laifuffukan kan iyaka
“Abu ne mai sauki a yi tunanin cewa mafita ita ce a karbe wadannan sabbin gwamnatocin soja da yin aiki da su saboda yaki da ta’addanci
Ministan Harkokin Kasashen Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi gargadi game da bayyana sauyin gwamnati da ake yi a yammacin Afirka a matsayin matsalar yanki kawai.
Tuggar ya kuma dage kan cewa juyin mulkin zai iya mamaye daukacin nahiyar Afirka tare da kara kalubalantar ta’addanci da sauran laifuffukan kan iyaka idan ba a magance su ba.