- Kotun kolin Najeriya ta ajiye hukuncinta kan takaddamar da ke tsakanin dan Takarar gwamnan APC, Air Marshal Sadeeq Baba Abubakar (mai ritaya) a zaben 2023 da kuma gwamnan jihar Bauchi mai ci, Bala Mohammed na PDP
- Dan Takarar gwamnan APC na fafatawa da hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben Mohammed na PDP
- Tuni Kotun koli ta bayyana cewa Nan Bada Jimawa Ba za ta Sanar da ranar da za ta Yanke Hukunci
Kotun kolin Najeriya ta ajiye hukuncinta kan takaddamar da ke tsakanin dan Takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadeeq Baba Abubakar (mai ritaya) a zaben 2023 da kuma gwamnan jihar Bauchi mai ci, Bala Mohammed na jam’iyyar PDP.
DAILY POST ta rahoto cewa Abubakar da APC na fafatawa da hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben Mohammed a kwanakin baya, bisa zargin karya dokar zabe.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince da Kasafin Kudin Shekarar 2024 na N270bn
Sun bukaci Kotun Koli ta soke hukuncin Kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben Mohammed.
A zaman da aka yi na ranar Alhamis, babban lauyan APC ya ce kotun daukaka kara ta yi watsi da muhimman batutuwa da suka hada da rashin bin dokar zabe a lokacin gudanar da zaben.
Sai dai Chris Uche, lauyan gwamna Mohammed, ya bukaci kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara, yana mai cewa ya dace da sashe na 148 da 135 na dokar zabe.
Bayan sauraron muhawarar daga bangarorin biyu, kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Inyang Okoro, ya bayyana cewa za a sanar da ranar da za a yanke hukunci ga dukkan bangarorin da abin ya shafa idan ya dace.
A wani labarin kuma,Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Amince da Kasafin Kudin 2024 Na N199.9bn
Majalisar dokokin Nasarawa ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 199.9
Kasafin idan gwamnan ya amince da shi zai inganta ci gaban tattalin arziki da ci gaban jihar
Bisa hakan shugaban majalisar, ya bukaci gwamnatin jihar da ta tabbatar da aiwatar da cikakken kasafin kudin
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 199.9 kamar yadda gwamna Abdullahi Sule ya gabatar.
Kakakin majalisar, Danladi Jatau, ne ya sanar da amincewa da kudirin dokar a yayin zaman majalisar a Lafia babban birnin jihar a ranar Laraba.