- Hukumar daukar ma’aikata ta ‘yan sanda ta amince da ranar 8 ga watan Janairu, 2024, a matsayin ranar da za a fara tantance wadanda suka yi nasara
- Hukumar ta gargadi ‘yan takarar da suka yi nasara da su yi taka-tsan-tsan da masu damfara
- Daukar ma’aikata kyauta ne ba’a Biyan ko sisi kuma za a yi la’akari da cancanta Ne kawai
Hukumar daukar ma’aikata ta ‘yan sanda ta amince da ranar 8 ga watan Janairu, 2024, a matsayin ranar da za a fara tantance wadanda suka yi nasarar daukarsu aiki a matsayin Jami’an ‘yan sanda na rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a Ikechukwu Ani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce hukumar ta gana a hedikwatar hukumar da ke Jabi, Abuja, inda ta dauki matakai da dama dangane da mataki na gaba na aikin daukar ma’aikata, Kamar yadda Daily Post ta rahoto.
KARANTA WANNAN: Mukaddashin Gwamnan Ondo Ya Gabatar da Kasafin N384.5bn Ga Majalisar Dokoki
“A lokacin da aka rufe tashar daukar ma’aikata a farkon wannan watan, an gano matasan Najeriya su kimanin 416,270 sun cika sharuddan farko na mataki na gaba na atisayen.
Sanarwar ta kara da cewa “Wadannan masu neman da Suka Yi nasara sun hada da Mutane 315,065 na aikin gama-gari da kuma 101,205 na kwararrun jami’ai,” in ji sanarwar.
A cewar sanarwar, ana sa ran ‘yan takarar da suka yi nasara za su sami wasikun gayyata a ranar 23 ga watan Disamba, 2023 ko kuma kafin nan.
“Wannan mataki na gaba na atisayen tantancewar zai hada da na zahiri da kuma na tantancewa da za a gudanar a jihar ta asali.
“Hukumar ta kuma ba da umarnin cewa ‘yan takarar da aka gayyata don tantancewar za su zo da asalin takaddun shaida da sauran takardun shaida, gami da wasikun shaida daga shugabannin kananan hukumominsu da/ko sarakunan gargajiya,” inji ta.
Sanarwar ta ce, sauran matakan daukar ma’aikata sun hada da jarabawar gwaji ta na’ura mai kwakwalwa wato CBT, wanda za a gudanar da shi bayan an kammala aikin tantancewa na zahiri da kuma duba lafiyar likitan a ranar da za a sanar da shi nan gaba kadan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A halin da ake ciki, bayan rufe tashar daukar ma’aikata, jihar Kaduna itace ke da mutane su dubu 31,117 da suka yi nasara kuma suke kan gaba, sai Adamawa Mai mutane 29,848; Benue, 25,346; Borno, 24,854; Katsina, 24,239; da kuma Bauchi, 22,958.
“Sauran jahohin da suka yi nasara sun hada da Kano, Mai yawan Mutane dubu 21,006; Neja, 17,959; Gombe, 17,493; Yobe, 17,207; Nasarawa, 16,284; Jigawa, 16,007; Taraba, 15,622; Plateau, 15,389 da kuma Jihar Kebbi, 12,917.”
Hukumar ta ce jihar Anambra, mai mutane 1,141, ita ce ta fi kowacce kasa a samun nasara a fadin kasar, sai Ebonyi, mai mutane 1,537; Legas, da 1,775; da Abia 2,110.
Sanarwar ta kuma gargadi ‘yan takarar da suka yi nasara da su yi taka-tsan-tsan da masu damfara, tana mai jaddada cewa daukacin aikin daukar ma’aikata kyauta ne kuma za a yi la’akari da cancanta da aiki.
A wani labarin kuma,Karon Farko a Matsayin Shugaban Kasa, Tinubu Ya Isa Legas Domin Bikin Kirsimeti
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya isa Legas domin hutun kirsimeti
Shugaban na Najeriya zai bi sahun mabiya addinin Kirista domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti
Tinubu ya Samu tarba Daga jiga-jigan Jami’an gwamnatinsa Dana Gwamnan Jihar ta Legas
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya isa jihar Legas ranar Alhamis domin hutun kirsimeti.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta samu cewa jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas da karfe 3:55 na rana.