- Wani tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande, ya bayyana banbancin dake tsakanin jam’iyyar APC da kuma PDP
- Gaskiya APC da PDP ba daya suke ba saboda sun fito daga wurare daban-daban
- Jam’iyyar PDP tana zuwa ne tun bayan shigar sojoji cikin harkokin mulki
Wani tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, ya bayyana banbancin dake tsakanin jam’iyyar APC da kuma jam’iyyar PDP.
Akande wanda shi ne Shugaban riko na farko a jam’iyyar APC, ya dage cewa jam’iyya mai mulki ba ta kama da PDP.
KARANTA WANNAN: Kirsimeti: Ganduje Ya Bayar Da Hutu Ga Ma’aikatan Jam’iyyar APC
Ya lura cewa PDP ta fito ne daga bangaren soja yayin da APC ke fitowa daga fagen tattaunawa, adawa, jarabawa da bita.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels TV, dattijon ya ce, “Gaskiya APC da PDP ba daya suke ba. Ba daidai ba ne saboda sun fito daga wurare daban-daban.
“Jam’iyyar PDP tana zuwa ne tun bayan shigar sojoji cikin harkokin mulki.
“Asalin shugabannin PDP sojoji ne, wadanda ba sa son barin mulki amma sai sun bar mulki ko wakilan sojoji, kamar ‘yan kwangilar da sojoji ke amfani da su a lokacin da suke kan mulki.
“Masu hankali na soji ne suka kafa jam’iyyar PDP, amma jam’iyyar APC ta fito ne daga bayan ‘yan adawa ga magadan sojoji a mulki.
“Sannan sojoji a harkokin mulki ba komai bane illa tarin rashin hukunta su..kowane shugaba yana aiki gwargwadon yadda kwakwalwarsa ke aiki.
“Amma gwamnatin farar hula na bukatar fahimtar gamayyar abubuwan da ya kamata a yi kuma ta hanyar muhawara akai-akai. Sojoji ba su da wurin muhawara.
“Dole ku bi umarni na ƙarshe, abin da maigida ya ce shi ne daidai, maigidan yana iya zama wawa amma duk umarnin da ya ba ku, dole ne ku yi biyayya …
“Don haka lokacin da kuka kawo su aikin gwamnati, tunanin ɓarna shine tushe saboda ba a basu horon mulki ba amma yaki…jimlar abin da sojoji da ke kan mulki suka yi na rashin adalci ne a mulki, PDP ta zo da wannan al’amari kuma haka suke mulki.
“Jam’iyyar APC ta zo da bangon tattaunawa, adawa, jarabawa, bita da kuma cewa ‘lafiya mu hadu mu zama kan mulki…”
A wani labarin kuma, Mutane Biyu Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Wani Ginin Beni Mai Hawa Biyu
Jami’an bayar da agajin gaggawa sun gano gawarwakin wasu mutane biyu, mace da namiji daga baraguzan ginin bene mai hawa biyu da ya ruguje
Tuni Jami’an bada a gajin gaggawa Suka dukufa don Ceto wadanda abin ya rutsa dasu
Jihar Legas dai ta Sha fama da iftila’in afkuwar rugujewar benaye a lokuta da Dama
Jami’an bayar da agajin gaggawa sun gano gawarwakin wasu matsakaitan mutane biyu, mace da namiji daga baraguzan ginin bene mai hawa biyu da ya ruguje da safiyar Juma’a a Ebute Meta da ke Legas.
Mista Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan Yankin Legas na hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN faruwar lamarin.