- Hukumar ba da lasisin barasa ta jihar Neja ta bayyana shirin hana sayar da barasa a Jihar
- Hukumar ta gargadin ma’aikatan hukumar da su nisanci ayyukan da suka sabawa doka da kuma neman biyan bukatun masu gudanar da gidajen giya
- Dola ne duk wasu dillalai su bi dokokin da suka dace da suka kafa hukumar saboda duk wanda ya bijirewa umarnin za a hukunta shi
Hukumar ba da lasisin barasa ta jihar Neja ta bayyana shirin hana sayar da barasa a garin Suleja da ke karamar hukumar Suleja ta jihar nan da ranar 1 ga watan Janairun 2024.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, wasu gidajen giyar da ke garin Minna, babban birnin jihar, za kuma a basu wasiku na komawa bayan gari zuwa wuri mai nisan kilomita takwas daga ofishin gidan waya a jihar.
KARANTA WANNAN: Gwamnonin PDP sun Taya Makinde Murnar Bikin Cikarsa shekaru 56 a Duniya
Sakataren hukumar Ibrahim Muhammad Bonu ne ya bayyana hakan a Minna.
Da yake gargadin ma’aikatan hukumar da su nisanci ayyukan da suka sabawa doka da kuma neman biyan bukatun masu gudanar da gidajen giya, Bonu ya ce duk ma’aikacin da aka samu yana so za a hukunta shi.
Ya ce: “Muna kira ga duk dillalai da su bi dokokin da suka dace da suka kafa hukumar. Dokar da ta kafa hukumar tana da hurumin kula da harkokin duk masu sayar da barasa a jihar don haka kananan hukumomi tara suka kasance a jadawalin farko na wuraren da aka haramta, kuma Suleja na cikin su, don haka hukumar ta kasance za ta tabbatar da bin doka sosai.”
A wani labarin kuma, Kirsimeti: Ku Yi Wa Tinubu Addu’ar Samun Nasara, Gwamnan Bauchi Ya Bukaci Kiristoci
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya bukaci mabiya addinin kirista a fadin kasar nan da su yi amfani da lokutan Kirsimeti wajen yi wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu addu’ar samun nasara
“Batun siyasa ya kare, lokaci ya yi da za a yi aiki, don haka yana bukatar addu’o’inmu na hadin gwiwa don samun nasara”
Addu’a na da matukar muhimmanci wajen sauya yanayi “Allah a shirye ya ke ya amsa addu’o’inmu. Mu yi wa gwamnatin tarayya addu’ar samun karin kudi domin ci gaba”
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya bukaci mabiya addinin kirista a fadin kasar nan da su yi amfani da lokutan Kirsimeti wajen yi wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara.
Gwamnan Bauchi ya jaddada cewa “batun siyasa ya kare, lokaci ya yi da za a yi aiki, don haka yana bukatar addu’o’inmu na hadin gwiwa don samun nasara. Ku yi masa addu’a kuma ku yi mini addu’a.”