- Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ba sun kashe akalla mutane 50 a wasu kauyuka na jihar
- Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ‘yan bindiga ke kai hare-hare da lalata gonaki da sauran kadarori a Jihar
- Tuni Dakarun Soji suka mayar da martani kan harin “A cikin sa’o’i 48 da suka gabata, sun amsa kiran gaggawa 36 daga wurare daban-daban a lokaci guda
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Litinin ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ba sun kashe akalla mutane 50 a wasu kauyukan kananan hukumomin Mangu da Bokkos na jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen liyafar cin abinci da babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar. Taoreed Lagbaja ya shirya ga sojojin Operation Safe Haven a Mangu.
KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Kuduri Aniyar Inganta Najeriya, Inji Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Ganduje
Mutfwang ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ‘yan bindiga ke kai hare-hare da lalata gonaki da sauran kadarori.
Ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai don magance matsalar rashin tsaro a jihar.
“A bayanan sirri da na samu, an kashe akalla mutane 50 a Mangu da Bokkos cikin sa’o’i 48 da suka gabata.
“Wannan ba abin yarda ba ne. Ya isa ya isa haka. Dole ne a daina waɗannan ayyukan wawanci da rashin hankali.
“Duk da haka, babu wani adadin hare-hare da zai karya ruhin mutanen Filato, mun tsaya tsayin daka da kuma kudurin ci gaba a matsayinmu na al’umma,” in ji shi.
Gwamnan ya godewa sojojin bisa jajircewar da suke yi wajen yaki da rashin tsaro a jihar sannan ya yi alkawarin tallafa wa sojoji da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron jihar.
“Ta haka ne za mu hana wasu ‘yan iska, wadanda galibi ke fakewa da hare-hare, daga aikata wasu laifuka, kamar satar shanu, fashi da makami, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da sauran laifuka.
“Za kuma mu karfafa sauran hukumomin tsaro don kara kaimi ga kokarin da sojoji ke yi wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar,” inji gwamnan.
A cikin jawabinsa, Kwamandan OPSH, Maj.-Gen. Abdusalam Abubakar ya ce dakarunsa sun mayar da martani kan harin.
Abubakar ya ce, “A cikin sa’o’i 48 da suka gabata, mun amsa kiran gaggawa 36 daga wurare daban-daban a lokaci guda.
“Yayin da muke magana, wasu daga cikin mutanenmu na kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka samu a hare-haren.
“Amma mun himmatu wajen ganin mun kawo karshen duk wasu laifuka a Filato,” inji shi.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: APC ta Fitar da Jadawalin Zabukan Cike Gurbi
Farashin fom ɗin nagani inaso da tsayawa takarar majalisar dattawa, Majalisar wakilai, da na majalisar dokokin jiha ya kai N20m, N10m, da kuma N2m
Wannan ya biyo bayan sanarwar da INEC ta yi na zaben cike gurbi na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi
Tuni mata Masu sha’awar neman takara da nakasassu za su sayi fom na nuna sha’awa yayin da fom din takara kyauta ne
Jam’iyyar APC ta Kaddamar da tsari da jadawalin ayyukan da za a gudanar na Zaben cike gurbi a ranar 3 ga watan Fabrairun 2024 mai zuwa.
Wannan ya biyo bayan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi na zaben cike gurbi na ‘yan majalisun tarayya da na jiha.