- Jami’ai sun ce an shatata ruwan sama kamar da bakin kwarya Inda aka bazama domin gano wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a wani lardin Afirka ta Kudu
- Bayan afkuwar ambaliyar, an yi hasashen za a samu karin mumunar guguwa a fadin lardin
- Wannan dai bashi ne karon farko da Yankin ya ke fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da bala’o’in yanayi a daidai lokacin da ake fama da yanayin zafi a duniya ba
Jami’ai sun ce an shatata ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata Inda aka bazama domin gano wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a wani lardin Afirka ta Kudu wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla bakwai tare da bacewar wasu 11.
Ambaliyar ruwa mai nisan mita 10 (kafa 33) ta ratsa wata gundumar Ladysmith, a lardin KwaZulu Natal, inda ta lalata gidaje tare da kwashe motoci, in ji masu ceto a cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar a ranar Talata.
KARANTA WANNAN: Gobara Ta Kone Shaguna 22 a Wata Kasuwa dake Jihar Kano
Hukumomin lardin sun tabbatar da mutuwar mutane 6 sannan wasu 10 sun bace.
Gaba dayan yankin kudu, wani kogin da ya mamaye Mandeni ya kwashe mutane uku. Hukumar ceto ta IPSS ta ce wani yaro dan shekara takwas ne aka tabbatar ya mutu sannan mutum daya ya bata.
Bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya an ci gaba da neman gawarwaki a Ladysmith mai tazarar kilomita 230 daga arewa maso yammacin birnin Durban, inda ruwan ya afku a yammacin Lahadi.
Tereza van den Berg, shugaban tawagar IPSS, ya ce kogin “a cikin zurfin mita 10” ya tsaga ta wani wurin shakatawa na ayari kuma ya yi awon Gaba da motocin da ke tsallaka gada.
“Babu wanda ya sami damar kama wani abu,” in ji ta. An gano wasu daga cikin motocin a nisan kilomita uku daga kasa.
An gano gawarwakin mutane uku a cikin wata karamar motar bas dauke da fasinjoji tara. Sauran shidan kuma har yanzu ba a gansu ba.
An tsinci gawa daya a cikin wani gida da ya ruguje yayin da wasu mutane biyu suma a ciki ba a gansu ba.
Akalla wasu mutane biyu ne suka mutu bayan da suka makale a cikin motocinsu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye kogin Bellspruit.
An yi hasashen za a samu karin mumunar guguwa a fadin lardin a ranar Talata.
KwaZulu Natal ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da bala’o’in yanayi a daidai lokacin da ake fama da yanayin zafi a duniya.
Fiye da mutane 450 ne suka mutu a ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa bayan wata mummunar guguwa ta afkawa Durban, babban birnin lardin, a watan Afrilun shekarar 2022.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Enugu Ta Sauya Shawarar Bude Gadar Da ta Ruguje
Gwamnatin Enugu ta ce ta dage bude titin Mai hanu daya daga cikin gadar babban titin Enugu zuwa Port Harcourt da ta ruguje
Tunda farko Gwamnatin Jihar ta tsara Bude Gadar domin masu ababen hawa su sami saukin zirga-zirga a lokacin bukukuwan kirsimeti dana Sabuwar Shekara
Ya kamata idan aka kammala, a yi gwajin ingancinta, domin tabbatar da ingancinta ga jama’a
Gwamnatin jihar Enugu ta ce ta dage bude titin Mai hanu daya daga cikin gadar babban titin Enugu zuwa Port Harcourt da ta ruguje bisa shawarar kwararru.
Gwamnati ta ce ta samu shawara daga manajan aikin, Mista Mohammed Fadi, da kada a sake bude gadar “don kare lafiya” har sai an kammala ta.