- Rundunar sojin Najeriya ta yi wa wasu sabbin manyan hafsoshi 47 ado da manyan mukamai na Manjo Janar
- Tuni rundunar ta bukace su da su kara kaimi wajen tunkarar kalubalen tsaro a a Najeriya
- karin girma da aka yiwa jami’an, shaida ce ta tsawon shekaru da suka kwashe suna aiki tukuru wajen yi wa kasa hidima
A ranar Alhamis ne rundunar sojin Najeriya ta yi wa wasu sabbin manyan hafsoshi 47 ado da manyan mukamai na Manjo Janar.
Rundunar ta bukace su da su kara kaimi wajen tunkarar kalubalen tsaro a kasar nan.
KARANTA WANNAN: Oyo: Gwamna Makinde Ya Ayyana Zaman Makoki na kwanaki Uku Bisa Mutuwar Akeredolu
Majalisar sojin kasar, a ranar 21 ga watan Disamba, ta amince da karin girma ga birgediya janar 47 zuwa mukamin Manjo Janar.
Majalisar ta kuma daga darajar Kanal 75 zuwa mukamin Birgediya Janar.
Za a yi wa sabbin birgediya-janar ado a sassansu da tsarinsu,Inji sanarwar
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce karin girma da aka yiwa jami’an, shaida ce ta tsawon shekaru da suka kwashe suna aiki tukuru da sadaukarwa wajen yi wa kasa hidima.
A cewarsa, ya bukaci jajircewa, da’a, da juriya kafin daga bisani su tashi daga mukaminsu, inda ya kara da cewa, dukkansu sun nuna kwarewa ta musamman na shugabanci, da tunani mai zurfi da kuma zurfin fahimta a yayin gudanar da ayyukansu.
“Gudunmawar da kuka bayar ga rundunar sojin Najeriya na da matukar kima, kuma muna da tabbacin za ku ci gaba da yi wa al’ummarmu hidima da daraja.
“Yayin da muka murnar ci gaban ku, ina roƙon ku da ku ci gaba da jagoranci ta hanyar misali da zaburar da wasu don inganta sawun ku,” in ji shi.
A halin da ake ciki, babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar. Taoreed Lagbaja, ya taya sabbin manyan hafsoshin sojan kasar da aka yi wa ado murna, inda ya ce karin girma da aka yi musu kyauta ne saboda kwazon da suka yi da kuma jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu.
Lagbaja ya kara da cewa, rundunar sojojin Najeriya a matsayinta na wani tsari na tada zaune tsaye, inda ya bukace su da su yi iya kokarinsu, bayan sun kai matakin tsara manufofin sojoji.
A wani labarin kuma,Bayan Binne Mahaifinsa Gwamnan Soludo Ya Koma Aiki, Ya Rattaba Hannun kan kasafin kudin 2024
Gwamnan Anambra Chukwuma Soludo ya koma bakin aiki bayan ya binne mahaifinsa Pa Simeon Soludo
Wannan dai na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da kasafin kudin ne jim kadan gabanin bikin Kirsimeti
Tuni dai gwamnan ya Rattaba hannu kan Kasafin Kudin Shekarar 2024 ya zama doka
Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo ya koma bakin aiki bayan ya binne mahaifinsa Pa Simeon Soludo.
Soludo bayan sake dawowa ya sanya hannu kan Kasafin Kudin Shekarar 2024 ya zama doka.