- Kamfanin da ke kan gaba wajen kera kayan sawa, Nike ya kaddamar da rigunan Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na gasar cin kofin kasashen Afrika
- Super Eagles na neman lashe kofi na hudu a wasan karshe na AFCON
- A shekara ta 2013 ne ‘yan wasan Najeriya suka doke Cote d’Ivoire da ci 2-1
Kamfanin da ke kan gaba wajen kera kayan sawa, Nike ya kaddamar da rigunan Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na gasar cin kofin kasashen Afrika na 2023 mai zuwa.
An tsara launin rigar ta Gida ta ‘yan wasan da launin kore da fari na Najeriya.
KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Amince da Bayar Da Kayan Agaji Don Tallafawa Wadanda Harin Filato Ya Shafa
Sannan an tsara rigar wanda tafi farin bango da yake taba kore.
Super Eagles na neman lashe kofi na hudu a wasan karshe na AFCON na 2023.
Kungiyar Jose Peseiro tana rukunin A ne da Cote d’Ivoire mai masaukin baki da Equatorial Guinea da kuma Guinea-Bissau.
A ranar 14 ga watan Junairu ne ‘yan Afirka ta Yamma za su fara wasansu da Equatorial Guinea a filin wasa na Alssanne Quattara da ke Ebimpe a Abidjan.
Za su kara da Cote d’Ivoire mai masaukin baki kwanaki hudu a wuri guda Wanda za’a Mai maita wajen sake buga wasan daf da na kusa da na karshe a shekara ta 2013, inda suka doke Cote d’Ivoire da ci 2-1.
Zasu kammala kamfen na rukunin A da fafatawar da zasu yi da Guinea-Bissau a ranar 22 ga watan Janairu.
A wani labarin kuma, Yobe: Gwamna Buni Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Kasafin Kudin 2024
Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kudi na shekarar 2024 ya zama doka
Wannan dai na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da shi
Ana saran kasafin kudin Zai sauya fasalin manufofin gwamnati na inganta rayuwar jama’ar jihar
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a ranar Alhamis ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kudi na shekarar 2024 bayan majalisar dokokin jihar ta amince da shi.
Buni, a yayin bikin rattaba hannun, wanda ya gudana a dakin taro na WAWA dake gidan gwamnati Damaturu, ya bayyana cewa rattaba hannu kan kasafin kudin ya yi daidai da sashe na 121 (1) da (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 kamar yadda aka gyara.