- Hukumar kidaya ta Najeriya ta yi rijistar haihuwa 424,302 a jihar Gombe tsakanin watan Janairu zuwa Nuwambar 2023
- Bayanan rajistar haihuwa na da matukar muhimmanci ga tsare-tsare da shiga tsakani na gwamnati
- Duk da yin rijistarar haihuwa hukumar ta koka da rashin yin rijistar mace-mace a jihar
Hukumar kidaya ta Najeriya ta yi rijistar haihuwa 424,302 a jihar Gombe tsakanin watan Janairu zuwa Nuwambar 2023.
Daga cikin wadanda aka yi wa rajista guda dubu 187,283 ko kashi 44.13 ‘yan mata ne yayin da guda dubu 237,019 ko kashi 55.86 maza ne.
KARANTA WANNAN: Firaministan Sipaniya Ya Nada Sabon Ministan Tattalin Arziki
Mista Adedeji Adeniyi, shugaban hukumar NPC’s Civil Registration and Vital Statistics a jihar Gombe ya bada cikakken bayani a ranar Juma’a a Gombe.
Ya ce rajistar da aka yi a cibiyoyin rajista sama da 100 da ke jihar ta shafi yara ‘yan tsakanin shekara 0 zuwa 17.
Ya ce Mutane dubu 76,900 daga cikin wadanda aka yiwa rajista yara ne ‘yan kasa da shekara daya, inda ya ce mutane dubu 33,760 daga cikinsu mata ne yayin da dubu 43,140 maza ne.
Ya ce ‘yan tsakanin shekara daya zuwa hudu sun kai su dubu 285,010, ya ce Mutane dubu 125,230 daga cikinsu mata ne, yayin da dubu 159,780 maza ne.
Wadanda ke tsakanin shekaru hudu da shekaru 17 sun kai yara dubu 62,392. ‘Yan matan sun kai 28,293 yayin da maza suka kai 34,099.
Adeniyi ya ce NPC ta kara daukar matakai tare da yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a jihar domin karfafa yin rijistar haihuwa.
Ya ce ta yi ƙaura daga tsarin rajistar haihuwa na Tsohon zamnai zuwa tsarin sabon zamani tare da haɗin gwiwar UNICEF.
Ya kara da cewa sauya sheka daga tsohon tsari zuwa na Wutar Lantarki ya sanya yin rijistar haihuwa ta zama matsala, sannan ya yi kira ga mazauna yankin da su yi rajistar haihuwarsu domin yin hakan, ya kara da cewa bayanan rajistar haihuwa na da matukar muhimmanci ga tsare-tsare da shiga tsakani na gwamnati.
Adeniyi ya jaddada cewa, “Yin rijistar haihuwa da takaddun shaida yana da mahimmanci don ba wa yara asalin zama ‘yan ƙasa da kuma damar samun abubuwan more rayuwa,” in ji Adeniyi.
Sai dai, duk da haka. ya koka da rashin yin rijistar mace-mace a jihar.
“Mazauna Gombe ba sa rajistar mutuwar ‘yan uwansu; kawai lokacin da suke son tattara wasu fa’idodi waɗanda ke buƙatar irin wannan takardar shaidar, sai su bayyana don irin wannan rajista.
“Ina kira ga mazauna garin da su yi rajistar mutuwar ‘yan uwansu domin hakan zai taimaka wa gwamnati wajen samun ingantaccen tsari na yanke shawara mai kyau kan abubuwan da ke faruwa a muhalli.
“Yin rijistar mace-mace yana ba da ra’ayin abubuwan da ke haifar da mutuwa kuma irin waɗannan ƙididdiga suna da mahimmanci don tsarawa kuma,” in ji shi.
Jaridar PUNCH ta rahoto cewa hukumar kidaya ta kasa ta ce ta samu kashi 57 cikin 100 na rijistar haihuwa ta zamani a fadin jihohi 23.
Daraktan, Vital Registration, NPC, Sunday Matthew, da yake zantawa da wakilinmu a watan Oktoban da ya gabata, ya jaddada bukatar iyaye su yi wa ‘ya’yansu rajista a lokacin haihuwa.
Ya ce, “Muna tattaunawa da iyaye musamman iyaye mata kan bukatar yin rijistar ‘ya’yansu a lokacin haihuwa.
“Muna sarrafa tsarin rajistar haihuwa don tabbatar da cewa ba za a yi rajista sau biyu ba.” NAN
A wani labarin kuma, NSCDC ta Yiwa Jami’anta 790 Ado da Aka Karawa Matsayi
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya reshen Legas, ta yi wa jami’anta 790 da aka kara wa girma ado a rundunar
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta umurci hukumar tsaro daban-daban da su kara wa jimillan ma’aikata 32,361 girma a dukkan mukamai
An shawarci jami’an da aka kara wa girma da su tabbatar da sabbin mukaman nasu da ayyukan kwarewa
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya reshen jihar Legas, ta yi wa jami’anta 790 da aka kara wa girma ado a rundunar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NSCDC na jihar, DSC Abolurin Oluwaseun, ya fitar a ranar Juma’a, an yi adon ne a ranar Alhamis a hedikwatar hukumar ta jihar, dake Alausa, Ikeja.