- Majalisar dattawa ta amince da kudirin kasafin kudin shekarar 2024, inda ta kara kasafin kudin daga Naira tiriliyan 27.5 zuwa Naira tiriliyan 28.7
- Hakan ya Sanya majalisar dattijai ta kara yawan kasafin kudin da kusan Naira Tiriliyan 1.2.
- Amincewa da kudirin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattijai kan kasafin kudi a zauren majalisar
Majalisar dattawa ta amince da kudirin kasafin kudin shekarar 2024, inda ta kara kasafin kudin daga Naira tiriliyan 27.5 da shugaba Bola Tinubu ya gabatar zuwa Naira tiriliyan 28.7.
Majalisar dattijai ta kara yawan kasafin da ake shirin yi da kusan Naira Tiriliyan 1.2.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Shugabannin Tsaro Kan Kisan Filato
Amincewa da kudirin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattijai kan kasafin kudi a zauren majalisa ranar Asabar.
Da yake gabatar da rahoton, Sanata Solomon Adeola ya ce kwamitin ya amince da tsarin kashe kudi na matsakaicin wa’adi da kuma takardar kudi, MTEF/FSP, wanda majalisar dokokin kasar ta amince da shi wajen shirya kasafin kudin.
Ya ce kwamitin ya amince da dala 77.96 kan kowacce gangar man Fetur mai lamba 1.78mbpd da dala 800 zuwa naira sabanin dala 750 da bangaren zartarwa ya gabatar.
Ya lissafa abubuwan da suka fi daukar hankali a cikin kudirin sun hada da jimillar kudaden da za’a kashe na Naira tiriliyan 28.7, da yadda doka ta tanada na Naira Tiriliyan 1.7, da kuma kudade da ake kashewa akai-akai na Naira Tiriliyan 8.7, yayin da bangaren kashe manyan kudade ya kai Naira Tiriliyan 9.9.
A cewarsa, kwamitin da ke tafiyar da kudirin ya yi aiki kafada da kafada da bangaren zartarwa.
Ya ce ta hanyar tsarin rabon kudaden da aka amince da su, hukumar zartarwa ta mika bukatar neman karin kudade na wasu abubuwa kan kashe kudade da ba a sanya su a cikin kudirin kamar yadda shugaban kasa ya gabatar ba.
Ya ce, duk da haka kwamitin ya lura cewa an gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin kasar a makare.
A wani labarin kuma,‘Dalilin Da Yasa Gwamna Mutfwang Ya Ziyarci Tinubu’ – Hadimin Gwamna
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan jihar Filato, Gyang Bere, ya fayyace dalilin ziyarar da gwamna Caleb Mutfwang ya kai wa shugaba Bola Tinubu
Makasudin ziyarar ita ce sanar da shugaban kasa matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a jihar
Wannan na zuwa ne bayan farmakin da aka kaiwa wasu al’ummomi da abin ya shafa a jihar
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan jihar Filato, Gyang Bere, ya fayyace dalilin ziyarar da gwamna Caleb Mutfwang ya kai wa shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin.
Ya ce makasudin ziyarar ita ce sanar da shugaban kasa matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a jihar da kuma neman shiga tsakani.