- Kwamitin gudanarwa, na jam’iyyar adawa ya dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Ondo, Fatai Adams
- An dauki matakin ne bisa ayyukan da ake zargin Shugaban PDP na yiwa jam’iyyar zagon kasa
- Matakin dakatar da shi ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar adawa ya dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Ondo, Fatai Adams.
A cewar SWC, an dauki matakin ne a kan ayyukan da ake zargin Adams na yiwa jam’iyyar zagon kasa da kuma kutsen da jam’iyyar APC mai mulki ta yi.
KARANTA WANNAN: Gwamna Abba Kabir Ya Magantu Kan Batun Naushin Sakataren Gwamnatin Kano
Wasikar dakatarwar wacce mambobin SWC tara suka amince da kuma sanya hannu, ciki har da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Jihar, Tola Alabere, Sakatare, Oluseye Olujim, da Sakataren Yada Labarai, Kennedy Peretei, sun bayyana cewa matakin da Adams ya ndauka kan jam’iyyar na da damar bata sunan jam’iyyar PDP a jihar.
Sauran wadanda suka sanya hannu a wasikar sun hada da sakataren shirya na kungiyar, Engr. Dare Akinwale; mataimakin shugaban Jam’iyyar na Ondo ta (Kudu), Elder Amos Fadope; Mataimakin shugaban Jam’iyyar na Ondo ta (tsakiya), Hon. Dayo Awode; mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Moses Awofade; Sakataren kudi, Hon. Boluwaji Hamidele; da Hon. Olawumi Fasonu, wanda shi ne ma’ajin.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa matakin dakatar da shi ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Bayan dakatarwar da aka yi wa Adams, an ba shi wa’adin mako guda ya bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar domin ya kare kansa daga zargin da ake masa.
“A bisa sashe na 58 (1b. c, f. h. da i) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP da aka yi wa gyara a shekarar 2017, kwamitin gudanarwa na jihar ya amince da dakatar da shugaban jam’iyyar na jiha, Mista Fatai Adams, kan wasu harkoki na adawa da jam’iyya da kuma gudanar da ayyuka Wanda mai yiyuwa ne su kawo wa jam’iyyar abun kunya.”
A wani labarin kuma, Gwamnati Gombe Ta Raba Kayan Abinci Ga ‘Yan Jihar 90k
Gwamnan Gombe, Muhammadu Yahaya, ya fara rabon kayayyakin jin kai zagaye na biyu ga mutane 90,000
Ya kamata a kai kayayyakin tallafin ga mabukata, marasa galihu da ke fama da talauci
Tuni dai yayin rabon kayayyakin wasu bata-gari suka yi awon gaba da wasu kayayyakin da aka raba
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya fara rabon kayayyakin jin kai zagaye na biyu ga mutane 90,000 a jihar.
Da yake jawabi jim kadan gabanin rabon kayan tallafin, Yahaya ya bayyana cewa akalla mutane 30 ne za su samu tallafin abinci a rumfunan zabe 2,998 da ke jihar.