- Hukumar NiMet ta fitar da sanarwar taka tsantsan ga mutanen da ke fama da cutar asma
- “Ya zama wajibi ga mutanen da ke fama da cutar asma da sauran matsalolin numfashi da su yi taka tsantsan game da yanayin”
- Ana sa rana samun yuwuwar saukar ruwan sama da tsawa a wasu sassan Najeriya
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta fitar da sanarwar taka tsantsan ga mutanen da ke fama da cutar asma da ta numfashi.
An kuma bayar da gargadin ne game da kurar hazo da gajimare da ke tafe ga ma’aikatan Jiragen Sama.
KARANTA WANNAN: NAF ta Amince da Tsarin Inshorar Hatsari Ga Ma’aikata
Rahoton NIMET ya kuma yi hasashen yanayi mai zafi tare da hasken rana da kurar hazo a jihohin Arewa da Arewa ta Tsakiya na kasar nan daga ranar Laraba 3 ga watan Janairu, 2024.
“An shawarci mutanen da ke fama da cutar asma da sauran matsalolin numfashi da su yi taka tsantsan game da yanayin”, in ji rahoton.
“An shawarci ma’aikatan jirgin sama da su sami sabbin rahotannin yanayi daga NiMet don ingantaccen shiri a ayyukansu.”
NiMet ta kuma yi kashedi game da gajimare da hazo, tare da karancin yiwuwar tsawa a kan yankunan gabar tekun Delta, Bayelsa da Rivers a lokutan rana da maraice.
Ta kuma yi bayani dalla-dalla cewa zuwa ranar Alhamis, “ana sa ran samun yanayi mai cike da rudani a yankunan Arewa da Arewa ta Tsakiya a duk tsawon lokacin hasashen.
Ana sa ran samun gajimare a cikin wani yanayi mai kurar hazo a yankunan Kudu da garuruwan da ke bakin teku tare da yiwuwar samun keɓancewar tsawa a sassan Rivers, Bayelsa da Delta da rana ko maraice.”
A ranar Juma’a an ce, “Ana sa ran samun yanayi na hasken rana da Hazo a yankin Arewa da Arewa ta Tsakiya a lokacin hasashen.
Sannan ana sa ran samun gajimare a cikin wani yanayi mai hazo a yankunan Inland, Kudu da gabar teku tare da yiwuwar tsawa a ware a sassan jihohin Edo, Bayelsa da Delta da rana da kuma maraice.”
A wani labarin kuma, Kalubalen Tsaro Zai Kawo Karshe Nan Bada Jimawa Ba — Gwamnatin Sokoto
Gwamnatin Sokoto ta jaddada kudirinta na magance matsalolin ‘yan fashi da makami da sauran matsalolin tsaro a jihar
Gwamnati a shirye take kuma ta dukufa wajen magance matsalolin da suka addabi al’umma
A baya dai rundunar Soji ta Mika mutane 66 da suka ceto daga hannun ‘yan bindiga ga gwamnatin jihar
Gwamnatin jihar Sokoto ta jaddada kudirinta na magance matsalolin ‘yan fashi da makami da sauran matsalolin tsaro a jihar.
Mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro Kanar Ahmed Usman (mai ritaya) shine wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilinmu kan wasu matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.