- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rattaba hannu kan sakin fursunoni 14 da aka zabo daga sassa shida na gidajen yarin jihar
- “A koyaushe ina bakin ciki idan na zo gidajen yari na ga fuskokin mutane masu hazaka
- An shawarci wadanda aka yiwa afuwar da su kasance masu halin kirki kuma su nuna kyakykyawan misali domin gwamnati ta zage damtse wajen sakin wasu fursunoni
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a ranar Alhamis ya rattaba hannu kan sakin fursunoni 14 da aka zabo daga sassa shida na gidajen yarin jihar.
Hakan dai ya yi dai-dai da yadda tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya ba shi ikon yin amfani da shi.
KARANTA WANNAN: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Min Rashin Adalci ~ Gwamnan Filato
Sule ya ce an gudanar da atisayen ne bayan tuntubar kwamitin ba da shawara kan hakkin jin kai, domin tabbatar da bin doka da oda da kuma kauce wa illa.
Ya ce, “A koyaushe ina bakin ciki idan na zo na ga fuskokin mutane masu hazaka, wasu daga cikin ku kanana matasa da ya kamata su fito su bayar da gudunmawar ci gaban jiharmu, musamman a irin wannan lokaci.
Da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban kanku da iyalanku.”
Ya kuma shawarci wadanda ke samun afuwar da su kasance masu halin kirki kuma su nuna kyakykyawan misali domin gwamnati ta zage damtse wajen sakin wasu fursunoni a cikin lokaci mai zuwa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnan ya amince da yin afuwa ga fursunoni 14 da ke zaman gidan yari daban-daban a cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya a jihar.
Kwamishinan shari’a na jihar, Labaran Magaji, a ranar Litinin, ya lura da matakin da gwamnan ya dauka na yin amfani da ikon da aka ba shi a karkashin sashe na 212 (1) da (2) na kundin tsarin mulki.
Ya bayyana sunayen fursunonin da suka hada da Sani Musa, Mohammed Maji, Danjuma Anthony, Ali Mohammed, Yahuza Turaki, Ibrahim Musa, da Abdullahi Usman.
Sauran sun hada da: ThankGod Ayaba, Usman Idris, Adamu Sule, Terzungwe Mshi, Shehu Abubakar, Zacheous Ayuba da Surajo Abdullahi.
Sashi na 212 (1) (a) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya ce gwamna na iya baiwa duk wanda ya shafi ko aka samu da laifin duk wani laifi da wata doka ta kafa ta jiha ta yi afuwa, walau kyauta ko kuma bisa sharuddan doka.
A wani labarin kuma,Mataimakiyar Gwamnan Adamawa ta Umurci ‘Yan Kwangila Da su Gaggauta Kammala Wasu Ayyuka
Mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta umurci ‘yan kwangila da ke gudanar da ayyukan gine-gine da su gaggauta Kammala aikin
Gwamnati tana mamakin dalilin da yasa aikin ke ci gaba da rarrafe. An fara wasu a baya amma an Kammala aikin
Gwamnatin jiha ba za ta lamunci duk wata lalura da ka iya kawo cikas ga kammaluwar aikin ba
Mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta umurci ‘yan kwangila da ke gudanar da ayyukan gine-gine a asibitin Lamurde Cottage dake kudancin jihar da su gaggauta Kammala aikin.
Haka kuma a babban asibitin Numan da ke kusa, mataimakiyar gwamnan wanda shima bata gamsu da yadda ake gudanar da ayyuka a wurin ba, ta bukaci ‘yan kwangilar da su tashi tsaye su cika sharuddan kwangilolin da suka kulla.