- Kotun kolin dai ta shirya sauraren kararraki 21 da suka shafi takaddamar zaben gwamna da aka gudanar
- Tuni dai jam’iyyu da magoya bayansu ke jiran wannan rana da sanin makomarsu
- Yanzu haka dai kowanne bangare na wadanda suke gaban kotun cikin su ya duri ruwa
Kotun kolin dai ta shirya sauraren kararraki 21 da suka shafi takaddamar zaben gwamna da aka gudanar a makon nan.
Za a saurari kararrakin da suka shafi jihohin Ebonyi, Plateau, Delta, Adamawa Abia, Ogun, Cross River da Akwa Ibom a tsakanin ranakun Litinin zuwa Alhamis.
KARANTA WANNAN: Zambar N585m: PDP ta Bukaci a Gurfanar Da Betta Edu A Gaban Kotu
Jaridar The Nation ta gano cewa kotun na iya yanke hukunci a karar da aka shigar gabanta na zaben gwamnan jihar Kano da Legas da sauran su ranar Juma’a.
Kamar yadda jadawalin kotun, wanda aka gani a yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu, kotun kolin ta shirya sauraren karar ranar litinin a wani daukaka kara da dan takarar jam’iyyar APGA, biyu na jam’iyyar PDP da dan takararta, Chukwuma. Odii Ifeanyi; da kuma daukaka kara biyu jam’iyyar APC da dan takararta a jihar Benue.
A ranar Talata ne kotun koli ta shirya sauraren kararraki shida – uku dangane da jihar Filato, wadanda jam’iyyar PDP da dan takararta, Nentawe Goshwe da INEC suka shigar; da uku dangane da jihar Delta, wanda Kenneth Gbagi na jam’iyyar SDP, Omo-Agege Ovie Augustine na jam’iyyar APC da kuma Peta Kennedy na jam’iyyar Labour Party (LP) suka shigar.
A ranar Laraba ne kotun ta shirya sauraren kararraki hudu, biyu dangane da jihar Adamawa, wanda dan takarar jam’iyyar SDP ya shigar da karar Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP (mai mulki).
Sauran biyun wadanda Okechukwu Ahiwe na PDP da Ikechi Emenike na APC suka shigar dangane da jihar Abia.
A ranar Alhamis, kotun ta shirya sauraron kararraki shida – biyu dangane da jihar Ogun da Oladipo Adebutu na PDP ya shigar da karar Abiodun na APC (gwamna mai ci); kan batun Cross River, wanda Farfesa Sandy Onor na PDP ya shigar; da biyu dangane da jihar Akwa Ibom, wanda Akpan Udofia na jam’iyyar YPP da John Akpan Udoedehe na NNPC suka shigar.
An tattaro cewa kotun na shirin yanke hukunci ne a ranar Juma’a, a kararrakin da aka yi na zaben gwamnan da aka riga aka yi, ciki har da na jihohin Legas, Kano da sauran su.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Sheikh Hasina ta Lashe Zabe Firaministar Kasar Bangladesh
Yanzu haka dai Sheikh Hasina ta sake lashe zaben Firaministan kasar Bangladesh
Tuni dai jam’iyyar Firaministan ta wawure rabin kujerun da aka kadawa kuri’a
An dai zabi Firaministan zuwa ga majalisa a karo na takwas tun shekarar 1986
Yanzu haka dai Sheikh Hasina a ranar Lahadi 7 ga watan Janairu ta sake lashe zaben Firaministan kasar Bangladesh a karo na biyar.
Tuni dai jam’iyyar Awami League ta Firaministan ta dauki akalla rabin kujeru kuma ana ci gaba da kirga kuri’un, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya rahoto daga wani Jami’in Zabe.