- An umarci dakatacciyar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara Dakta Betta Edu da ta kai kanta zuwa hedikwatar hukumar EFCC
- Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Ministar kan badakalar zunzurutun kudi Naira miliyan 585
- Hakan ya biyo bayan Gayyatar da EFCC ta yi wa ministar bisa bin umarnin Tinubu na a gudanar da cikakken bincike da ya kunshi ayyukanta a ma’aikatar
An umarci dakatacciyar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara Dakta Betta Edu da ta kai kanta zuwa hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da ke Jabi, Abuja a ranar Talata, 9 ga watan Janairu.
A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Edu kan badakalar zunzurutun kudi Naira miliyan 585.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Taraba Kefas Ya Musanta Tsoma Baki A Zaben Cike Gurbi.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyaci ministar ne bisa bin umarnin Tinubu na a gudanar da cikakken bincike da ya kunshi ayyukanta a ma’aikatar, kamar yadda wata majiya mai karfi a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shaida wa manema labarai.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu, Monday wani babban jami’in hukumar ta EFCC ya ce, “An umarci Betta Edu ta kai kanta ga hukumar (EFCC) gobe.”
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa har yanzu magabaciyar Edu, Sadiya Farouq, hukumar EFCC na cigaba da yi mata tambayoyi da misalin karfe 6:40 na yammacin ranar Litinin, bisa zargin ta da karkatar da naira biliyan 37.1 a lokacin da take rike da mukamin minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A wani labarin kuma, Gwamnan Kogi Yahaya Bello Ya Kori Sarakunan Gargajiya Hudu, Ya Yi Sabon Nadi
Gwamnatin Kogi ta kori sarakunan gargajiya hudu da suka hada da wani basaraken mai daraja ta daya
Tuni Gwamnatin Jihar ta bada Umarnin fitar da Sarakunan Gargajiyar daga jihar zuwa wani wuri
Bayan bin dokokin gargajiya da na masarautu, da ka’idoji da tsare-tsaren da suka dace, an cimma matsayar da katar da su
Gwamnatin jihar Kogi ta kori sarakunan gargajiya hudu da suka hada da wani basaraken mai daraja ta daya, Ohimege Igu, Konto-Nkarfe, da Alhaji Abdulrazaq Koto.
Daga nan aka mayar da Koto zuwa karamar hukumar Rijau ta jihar Neja.