- Kotun koli za ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar da gwamnan jihar Kano
- Wannan ya biyo bayan karar da gwamnan Kano ya shigar kotun koli
- An dai jima ana jiran wannan rana
Kotun koli za ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar da gwamnan jihar Kano.
Gwamnan jihar, Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP yana kalubalantar hukuncin da wata karamar kotu ta yanke wanda ta soke zabensa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Gwamnan Bauchi Bala Mohammed
Mai shari’a John Okoro na karanto hukuncin da aka yanke har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
A wani labarin kuma, Kotun Koli Za ta Yanke Hukunci Kan Makomar Gwamnoni Takwas a Gobe Juma’a
A ranar Juma’a ne kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan zaben gwamnonin jihohi takwas
Gwamnonin Takwas suna fuskantar zazzafar hamayya daga jam’iyyun adawa wajen ganin sun rabasu da Kujerun su
Zuwa yanzu dai cikin Kowanne mai kara da wadanda suka shigar da kara ya duri ruwa
A ranar Juma’a ne kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan zaben gwamnonin jihohi takwas da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Gwamnonin da kotun koli za ta yanke hukunci kan makomarsu su ne na Kano, Abba Kabir Yusuf; Bauchi, Bala Mohammed; Plateau, Caleb Mutfwang; Ebonyi, Francis Nwifuru; Cross River, Bassey Otu; Lagos, Babajide Sanwo-Olu; Jihar Zamfara, Dauda Lawal da kuma Abia, Alex Otti.