- Wata kungiyar matsa a cikin jam’iyyar PDP ta yi kira ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, da kada ya sake tsayawa takara
- CPDPL ta bukaci shugaban kungiyar gwamnonin PDP da kada ya sanya wani buri na neman kujerar shugaban kasa har sai shekarar 2031
- Ya da kyau jam’iyyar ta yi taka-tsan-tsan da abubuwan da suka haddasa faduwarta a babban zaben 2023
Wata kungiyar matsa a cikin jam’iyyar PDP, wato Concerned PDP League, CPDPL, ta yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023, da kada ya sake tsayawa takara a shekarar 2027.
Shawarar kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka sanya wa hannu a ranar Lahadi kuma aka fitar a Abuja ta hannun sakatarenta na kasa, Alhaji Tasiu Muhammed da kuma mukaddashin daraktan yada labarai da sadarwa na kasa, Gbenga Adedamola.
KARANTA WANNAN: Ni Jarumi Ne, Ba Na Tsoron Fada – Gwamnan Bauchi Bala Muhammed
CPDPL ta kuma bukaci shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, da kada ya sanya wani buri na neman kujerar shugaban kasa har sai 2031, don kaucewa sake afkuwar abin da ya faru da jam’iyyar a shekarun 2015 da 2023.
A cewar kungiyar, shawarar da ta bayar ya kasance masu sha’awar tsayawa takara daga Arewa su fahimci cewa Kudu tana da sauran shekaru takwas kafin mulki ya dawo Arewa a 2031.
“Shawarar mu kuma ita ce tabbatar da kwanciyar hankali a tsarin siyasar kasar,” in ji kungiyar.
Ta kuma shawarci jam’iyyar da ta yi taka-tsan-tsan da abubuwan da suka haddasa faduwarta a babban zaben 2023, tare da kauce musu yayin da take shirin tunkarar zaben 2027.
“Kamar yadda muka sani, shekarar 2023 shekara ce mai matukar kalubale ga babbar jam’iyyarmu, inda muka sha kaye a zaben shugaban kasa saboda rashin bin kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu na 2017, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, da gazawar shugabanci,” in ji CPDPL.
A wani labarin kuma, Hukuncin Kotun Koli: Jam’iyyar Adawa ta APC ta Taya Gwamnan Filato Mutfwang Murna
Shugaban Jam’iyyar Adawa ta APC a jihar Filato, Hon Rufus Bature ya taya gwamnan jihar Caleb Mutfwang murnar nasarar da ya samu a kotun koli
Nasarar da ya samu bayan an dade ana tafka shari’a ta kawo karshen wanene ainihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar
Ya kamata Gwamnan ya yi duba ga wasu matakan gaggawa da ya dauka dangane da batun korar ma’aikatan da magajinsa ya dauka aiki
Shugaban jam’iyyar adawa ta APC a jihar Filato, Hon Rufus Bature ya taya gwamnan jihar Filato Barista Caleb Mutfwang murnar nasarar da ya samu a kotun koli.
Jam’iyyar adawar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta Mista Slyvanus Namang ta ce nasarar da gwamna Caleb Mutfwang ya samu bayan an dade ana tafka shari’a ta kawo karshen wanene ainihin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Filato a shekarar 2023.