- Shugaban kasa Tinubu ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
- Duk da ziyarar Tinubu, Obasanjo ya goyi bayan jam’iyyar Labour Party LP
- A baya dai Tinubu da Obasanjo sun sha fama da tsamin dangantaka
A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya rungumi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tare da yin musabaha.
Mutanen biyu sun gana ne a yayin rantsar da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo a Owerri a karo na biyu.
KARANTA WANNAN: An Rantsar Da Uzodimma A Matsayin Zababben Gwamnan Imo Na 7
A baya dai Tinubu da Obasanjo sun sha fama da tsamin dangantaka amma sai suka ga kamar sun gyara shinge kafin zaben shugaban kasa na 2023 a lokacin da ya ziyarci tsohon shugaban kasar a Ota, jihar Ogun.
Duk da ziyarar Tinubu, Obasanjo ya goyi bayan jam’iyyar Labour Party, LP, dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, a lokacin zaben da ya gabata.
A wani labarin kuma, Nasarawa: PDP da APC Sun Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Zaman Lafiya Gabannin
Rundunar ‘yan sandan Nasarawa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da shugabannin jam’iyyar PDP da na APC
“Wannan taron an yi shi ne da nufin tabbatar da zaman lafiya kafin yanke hukuncin kotun koli da lokacin da kuma bayan yanke hukuncin
“Duk wanda ya saba wa wannan yarjejeniya ta zaman lafiya, komai girman matsayin sa a cikin al’umma zai yi nadamar matakin da ya dauka.”
Yayin da mazauna jihar Nasarawa ke hasashen hukuncin kotun koli kan zaben gwamna na 2023, rundunar ‘yan sandan jihar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da shugabannin jam’iyyar PDP da na APC a jihar.
A lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Lafiya a ranar Litinin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Nadada, ya sha alwashin hukunta duk wanda ya shiga cikin kowace irin matsala kafin yanke hukunci, da lokacin da kuma bayan yanke hukunci.