- Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Emmanuel Ukpong-Udo a matsayin dan majalisar wakilai a jihar Akwa Ibom
- Kotun daukaka karar ta ce matakin da INEC ta dauka na bayyana dan Majalisar a matsayin wanda ya lashe zaben ya saba wa dokar zaben 2022
- An fara zaben dan majalisar wakilan a shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar PDP, amma daga baya ya koma YPP
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Emmanuel Ukpong-Udo a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikono/Ini ta jihar Akwa Ibom.
Kotun daukaka kara ta ce matakin da INEC ta bayyana Mista Ukpong-Udo a matsayin wanda ya lashe zaben ya saba wa dokar zabe ta shekarar 2022, dokoki da ka’idoji na gudanar da zaben 2022 da kuma littafin jagorar zaben 2023.
KARANTA WANNAN: Bola Tinubu Ya Rantsar da Shugaban PDP a Babban Muƙamin Gwamnati
Alkalin kotun, Abba Mohammed, ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta kori Mista Ukpong-Udo, dan takarar jam’iyyar YPP a zaben 2023.
Mista Ukpong-Udo dai ya kayar da babbar abokiyar hamayyarsa Glory Edet ta jam’iyyar PDP a zaben.
‘Yar takarar YPP ta samu kuri’u 19,926 inda ta doke ‘yar takarar PDP Mrs Edet wacce ta samu kuri’u 15,765.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa kuri’un na karshe sun fito ne sakamakon hadakar sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da na ranar 15 ga watan Afrilu 2023.
INEC ta ayyana zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a yankin da bai kammalu ba kuma ta sanya ranar 15 ga watan Afrilun 2023 domin sake gudanar da zaben.
Hukumar ta sake soke zaben Inda ta kara da cewa ya kasance da tashin hankali da sace akwatin zabe.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa kotun daukaka kara ta bayar da umarnin sake gudanar da zaben, sai dai babu tabbas ko an bayar da umarnin sake gudanar da zaben ne a daukacin mazabar tarayya ko kuma a rumfunan zabe da hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa sakamakon bai kammala ba.
An fara zaben Mista Ukpong-Udo ne dan majalisar wakilai ta kasa a shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar PDP, amma daga baya ya koma YPP ya samu tikitin jam’iyyar bayan ya kauracewa zaben fidda gwani na PDP.
A wani labarin kuma, Rundunar ‘Yan sandan Nasarawa Ta Ba da Umarnin Tsaurara Tsaro A Kan Iyakokin Abuja
Kwamishinan ‘yan sandan Nasarawa, CP Umar Shehu Nadada, ya bayar da umarnin tura isassun jami’an ‘yan sanda da ’yan banga zuwa yankunan da ke kan iyaka da Abuja
Tura jami’an ya zama dole saboda matsalolin tsaro da ake fama da su a fadin kasar nan
Bisa hakan ba za a amince da duk wani lalaci da rashin da’a ba
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa, CP Umar Shehu Nadada, ya bayar da umarnin tura isassun jami’an ‘yan sanda da ’yan banga zuwa yankunan da ke kan iyaka da babban birnin tarayya, FCT, Abuja.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nasel ya fitar ranar Laraba.