- Mambobin kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU, na jami’ar jihar Abia, Uturu, sun dakatar da yajin aikin da suke yi
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan ya nuna jajircewarsa wajen biyan bukatun kungiyar
- A kwanakin baya shugaban gudanarwar jami’ar ya roki mambobin kungiyar ASUU su janye yajin aikin
Mambobin kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU, na jami’ar jihar Abia, Uturu, sun dakatar da yajin aikin da suke yi kwanaki bakwai bayan sun kakkabo kayayyakin aiki.
Kungiyar ta dakatar da ayyukan masana’antu ne bayan ta gudanar da taron gaggawa a yau a babbar harabar jami’ar da ke Uturu, inda ma’aikatan makarantar suka yanke shawarar komawa aji.
KARANTA WANNAN: Kotu Ta Umurci ‘Yan Sanda Su Biya Matar MKO Abiola Diyyar Miliyan 50
Shugaban kungiyar ASUU na jami’ar, Dakta Chidi Slessor Mba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Gwamna Alex Otti ya nuna jajircewarsa wajen biyan bukatun kungiyar da suka shafi neman bashin albashin watanni 11 da dai sauransu ta hanyar gayyato su don tattaunawa.
Mbah ya bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnan zai biya bukatun kungiyar cikin gaggawa.
A halin da ake ciki, wasu daliban makarantar da suka dawo daga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara, sun ce janye yajin aikin wani albishir ne a gare su, domin zai gurbata kalandar karatunsu.
DAILY POST ta tuna cewa a kwanakin baya shugaban hukumar gudanarwa na jami’ar jihar Abia Mba Ukariwo ya roki mambobin kungiyar ASUU da su janye yajin aikin da suka shiga domin tattaunawa kan kokensu.
A wani labarin kuma, Babu Wani Aiki Da Zai Tsaya A Karkashin Gwamnatin Tinubu – Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bada tabbacin cewa babu wani aiki da zai tsaya a karkashin shugaba Tinubu
Akwai da yawa daga cikin waɗannan rukunin, amma zai yi wahala ɗaukar su duka a lokaci guda
“Mun yi imanin cewa bayan watan Mayu, da kuma kafin watan Disamba, za a mika wasu ayyukan ga jama’a
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bada tabbacin cewa babu wani aiki da zai tsaya a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Wike ya bayyana fatan cewa, wasu daga cikin ayyukan da ake ci gaba da yi za a kammala su kuma Tinubu ya kaddamar da su kafin watan Disambar 2024.