- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan yadda hukumar Hisbah ta jihar ke kasa shawo kan matsalar rashin da’a a jihar
- Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya yi alkawarin sake farfado da hukumar domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata
- Ma’aikatar ta himmatu wajen kara kaimi ga kokarin gwamnan na magance duk wasu munanan dabi’u a jihar
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan yadda hukumar Hisbah ta jihar ke kasa shawo kan matsalar rashin da’a da rashin zaman lafiya a tsakanin matasa da kananan yara a jihar.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya yi alkawarin sake farfado da hukumar domin baiwa hazikan mutane damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
KARANTA WANNAN: APC ta Lashe Zaben Dukkan Kujerun Kananan Hukumomin Jihar Borno
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron manyan limamai daga masallatan Juma’a daban-daban a cikin babban birnin Bauchi ranar Lahadi.
Muhammed ya kara da cewa ana shirin nada manyan mataimaka na musamman daga kungiyoyin addinin musulunci da na kiristoci daban-daban domin cigaba da marawa kudirin gwamnati baya na sake fasalin al’umma.
Yayin da yake nuna rashin gamsuwa da wa’azin da wasu malaman addini suke yi, gwamnan ya ja hankalin malaman addini da su yi amfani da iliminsu wajen inganta ingantacciyar koyarwar addininsu.
Da yake jawabi a madadin tawagar, kwamishinan harkokin addini, Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza, ya bayyana matakin na sauya hukumar ta Hisbah a matsayin mataki mai kyau.
Ya ba da tabbacin ma’aikatar ta himmatu wajen kara kaimi ga kokarin gwamnan na magance duk wasu munanan dabi’u a jihar Bauchi.
A wani labarin kuma, Zazzabin Lassa: Mutane 227 Sun Mutu Yayin Da Sama Da 1k Suka Kamu Da Cutar
Akalla mutane 227 ne suka mutu sannan 1,270 aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin Lassa a Najeriya
Hakan ya biyo bayan samu bullar cutar a jihohi 28
Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa ta Zazzabin Lassa za ta karfafa hadin gwiwar kokarin mayar da martani don rage yaduwar cutar
Akalla mutane 227 ne suka mutu sannan 1,270 aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin Lassa a Najeriya daga jihohi 28 a shekarar 2023.
Wannan sanarwar ta fito kamar yadda Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta fitar.