- Gwamnan Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya amince da bayar da tallafin kudin jarabawar kammala karatu na matakin farko (BECE) na shekarar 2024 ga dalibai
- Tallafin na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na tallafa wa daliban da iyayensu don Kau cewa daina zuwa makaranta
- Gwamnati ta gargadi jami’an gwamnati da su guji karbar kudade daga hannun iyaye ta kowace hanya
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya amince da bayar da tallafin kudin jarabawar kammala karatu na matakin farko (BECE) na shekarar 2024 ga dalibai a makarantun gwamnati dake fadin jihar.
Wannan dai na zuwa ne ya yin da ‘yan takara 55,150 ne ke rubuta jarabawar a jihar Kwara.
KARANTA WANNAN: Sabon Shugaban Kasar Laberiya, Boakai Ya Sha Wani Alkawari Bayan Rantsar da Shi
Wata sanarwa da ma’aikatar ilimi da ci gaban bil’adama ta jihar ta fitar ta hannun sakataren yada labarai a ma’aikatar, Peter Amogbonjaye, ta ce duk daliban dake makarantun gwamnati za su biya Naira 2,500 kacal, kudin da aka karba a bara maimakon Naira 5,000 ko kuma fiye da wanda aka so a sake duba shi saboda hauhawar farashin kaya da tsadar gudanar da jarrabawar.
Sanarwar ta ce tallafin na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na tallafa wa daliban da iyayensu, tare da kaucewa duk wani dalibi da ya daina zuwa makaranta saboda rashin samun kudin jarabawar.
Har ila yau, ya ce tallafin zai samu ne daga dukkan ‘yan takarar da za su zauna rubuta wannan jarabawa ta BCE a shekara ta 2024.
Don haka sanarwar ta gargadi jami’an gwamnati da su guji karbar kudade daga hannun iyaye ta kowace hanya, tana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci sakamakon irin wannan mataki.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Soke Kasafin Kudin Jihar Ribas Na 2024
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta soke kasafin kudin Jihar Ribas na 2024
Alkalin Kotun ya ce kasafin kudin bai yi aiki ba saboda ba a gabatar da shi yadda ya kamata a gaban majalisar dokokin jihar ba
Kotun ta zargi Gwamnan da yin katsalandan a cikin harkokin majalisar dokokin jihar
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta soke kasafin kudin Jihar Ribas na shekarar 2024.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a James Omotosho, ya yanke a ranar Litinin, ta ce kasafin kudin bai yi aiki ba saboda ba a gabatar da shi yadda ya kamata a gaban majalisar dokokin jihar Ribas.