- An dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Dekina a jihar Kogi, Ibrahim Huseini
- Ayyukan Shugaban sun kawo cikas ga ci gaban jam’iyyar ta hanyar kin bin tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar
- Tsige Shugaban jam’iyyar ya samu taron dangi daga jiga-jigan jam’iyyar ta PDP
An dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Dekina a jihar Kogi, Ibrahim Huseini har sai baba ta gani.
Huseini, kafin dakatarwar da aka yi masa, an zarge shi da karkatar da Naira miliyan 19 daga asusun jam’iyyar da kuma yin barazana ga mambobin jam’iyyar.
KARANTA WANNAN: Yadda Sabon shugaban Kasar Laberiya, Boakai Ya Kasa Kammala Jawabin Rantsar da Shi
Haka kuma an zarge shi da aikata ayyukan kin jinin jam’iyya a zaben gwamnan da ya gabata a watan Nuwambar shekarar 2023.
Dakatar da Huseini na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Junairu, 2024, inda jami’an jam’iyyar PDP na karamar hukumar Dekina suka kada kuri’ar rashin amincewa da shugaban.
Kwamitin gudanarwa na karamar hukumar PDP a Dekina ya zargi shugaban da rashin mutunta ka’idojin jam’iyyar da aka kafa.
Wasikar ta ci gaba da cewa: “Mu shugabannin kananan hukumomi da na mazabu na karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi, mun dakatar da ku a matsayin shugaban jam’iyyar a ranar 15 ga watan Junairu, 2024, biyo bayan kuri’ar rashin amincewa da mafi rinjayen zartarwa a kananan hukumomi suka yi.
“Wannan shawarar ta samo asali ne daga yadda ku ke karkatar da kudaden jam’iyya, da bayyana barazana ga mambobin zartarwa, da kuma shigar da jam’iyyar gaba a zaben shugaban kasa da na gwamnonin jahohi da ya gabata a jihar.
“Ana umartar ku da ku mika dukkan kayan jam’iyyar da ke hannunku ga sakataren sashe na jam’iyyar. Ayyukanku sun kawo cikas ga ci gaban jam’iyyar ta hanyar kin bin tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.”
Daga cikin wadanda suka rattaba hannun amincewa da kada kuri’ar a matakin kananan hukumomi da mazabu, akwai Sakatare Ademu Yusuf, Mataimakin Sakatare Attai Joseph, mai ba da shawara kan harkokin shari’a Jacob Atadoga, mai binciken kudi John Bala Amedu, Sakataren kudi Usman Enema, Ma’ajin Salisu Shehu, Shugaban Matasa Ayuba da sauransu.
Sauran sun hada da shugabar mata Alima Abuh da mataimakiyar shugaba Salami Muhammed Omede.
Akalla shugabannin unguwanni takwas ne suka amince da tsige shi.
A wani labarin kuma,‘Yan Majalisar Dokokin Filato 16 Da Aka Kora Sun Sha Alwashin Komawa Bakin Aiki
Yayin da majalisar dokokin Filato za ta koma zamanta a ranar Talata, ‘yan majalisar wakilai 16 da aka zaba a PDP sun ce za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na majalisar
‘Yan majalisar da ke cikin rudani sun bayyana takaicin su kan yadda alkalan kotun daukaka kara suka yanke hukuncin korarsu daga aiki
‘Yan Majalisar da Kotu Ta Kora sun yi kira ga wadanda suka ci gajiyar hukuncin kotun daukaka kara da kada su dauki kan su a matsayin ‘yan majalisa domin ba jama’a ne suka zabe su ba
Yayin da majalisar dokokin jihar Filato za ta koma zamanta a ranar Talata, ‘yan majalisar wakilai 16 da aka zaba a dandalin jam’iyyar PDP a ranar Litinin sun ce za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na majalisar duk da korar da kotun daukaka kara ta yi.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a watan Nuwambar shekarar da ta gabata ta 2023 ta kori dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar su 16 da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP bisa hujjar cewa jam’iyyar ba ta da tsarin tantance su a matsayin ‘yan takara.