- Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da ayyukan da ake bukata a harkar man fetur da iskar gas
- Shugaban ya bayyana hakanne a yayin da yake jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga
- Shugaba Tinubu ya ce Najeriya za ta karfafa dangantakar da ke tsakaninta da kamfanin na kasa-da-kasa
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da ayyukan da ake bukata a harkar man fetur da iskar gas kamar yadda dokar masana’antar man fetur ta PIA ta tanada.
Shugaban ya bayyana hakanne a yayin da yake jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga karkashin jagorancin Mista Clay Neff, shugaban kamfanin Chevron International Exploration and Production, a ranar Talata a Abuja.
KARANTA WANNAN: Gwamna Buni Ya Mayar Da Martani Kan Afkuwar Gobarar Kasuwar GSM ta Damaturu
Shugaba Tinubu ya ce Najeriya za ta karfafa dangantakar da ke tsakaninta da kamfanin na kasa-da-kasa, bisa la’akari da ci gaban da ake samu a harkar man fetur da kuma samar da man fetur da masana’antar iskar gas.
Shugaban ya yi maraba da kudirin Chevron na bunkasa jarin da yake zubawa a ayyukan ruwa mai zurfi a Najeriya, inda ya yi nuni da aikin hako mai na dala biliyan 1.4 da kamfanin ke yi tare da Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL.
Ya kuma ya bawa kamfanin Chevron bisa jajircewarsa na rage yawan iskar carbon da yake fitarwa a kasar.
“Dole ne ku kalli PIA a matsayin doka ta gado. Muna ba ku tabbacin yin gaggawar shiga tsakani da juyowa kan duk wata matsala da kuke da ita a cikin ayyukanku a cikin ƙasarmu.
“Najeriya na alfahari da hadin gwiwa na shekaru 60 da kamfanin Chevron, kuma mun yi imanin za a karfafa wannan hadin gwiwa don kara amfani da moriyar juna domin amfanin masu hannun jarin ku da kuma yanayin rayuwa da damar tattalin arzikin al’ummarmu,” in ji Shugaba Tinubu.
A nasa jawabin, Mista Neff ya yi alkawarin cewa kamfanin zai ci gaba da gudanar da ayyukansa bisa manyan tsare-tsare, duk da cewa ya cika alkawuran zuba jari a Najeriya.
Ya bayyana irin gudunmawar da kamfanin ke bayarwa wajen samar da iskar gas a cikin gida, inda ya bayyana cewa isar da kashi 25 cikin 100 na iskar gas ta hanyar hadin gwiwa da kamfanin NNPC Limited.
A wani labarin kuma, Gwamna Abiodun Ya Rantsar da Sabbin Alkalai Uku da Wasu Manyan Sakatarori
Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya rantsar da Mista Martins Akinyemi a matsayin alkalin babbar kotun jihar
Gwamnan ya tuhumi sabbin alkalan da aka rantsar a jihar da su zama fata na karshe na talaka
A cewar Gwamnan anyi hakan ne don Tabbatar da adalci da doka, da oda, da gaskiya domin inganta rayuwar mutane ta hanyar samun daidaiton
A ranar Talata ne gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya rantsar da Mista Martins Akinyemi a matsayin alkalin babbar kotun jihar.
Sannan gwamnan ya rantsar da Mrs. Bolanle Awoyemi da Mista Adeniyi Lawal a matsayin alkalan kotun Kwastomari.