- Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya nada Cif Olayide Owolabi Adelami a matsayin mataimakin gwamnan
- Wannan na Zuwa ne ‘yan sa’oi kadan bayan da Gwamnan ya rusa majalisar zartarwa ta jihar
- Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar bayan rasuwar Rotimi Akeredolu
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya nada Cif Olayide Owolabi Adelami a matsayin mataimakin gwamna a hukumance.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar Ondo bayan rasuwar Rotimi Akeredolu.
KARANTA WANNAN: Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu Ya Shilla Kasar Waje
Akeredolu ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disambar shekarar 2023, a wani asibitin kasar Jamus sakamakon doguwar jinya.
Wannan na Zuwa ne ‘yan sa’oi kadan da Gwamnan na Ondo Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwa ta jihar
Gwamnan ya kuma sauke dukkan manyan mataimaka na musamman da mataimaka na musamman daga ayyukansu.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Ebenezer Adeniyan ya fitar a ranar Laraba, gwamnan ya ce ci gaban zai fara aiki nan take.
Sanarwar ta ce, “Dukkan mambobin majalisar za su mika ayyukan su ga manyan sakatarorin ko kuma manyan jami’an gudanarwa a ofisoshinsu.
“An umurci dukkan jami’an da abin ya shafa da su mika duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu.
“Gwamnan ya godewa jami’an da abin ya shafa bisa ayyukansu da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Gwamnan Ondo Aiyedatiwa Ya Kori Kwamishinoni Da Hadiman Gwamna
Gwamnan Ondo Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwa ta jihar
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Gwamnan ya fitar
Jim kadan gabanin rantsar da Gwamna Aiyedatiwa, mai ba Akeredolu shawara kan harkokin kungiyar da ayyuka na musamman da babban sakataren yada labarai sun yi murabus
Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwa ta jihar.
Gwamnan ya kuma sauke dukkan manyan mataimaka na musamman da mataimaka na musamman daga ayyukansu.