- Kotun kolin kasar ta yi watsi da daukaka karar da tsohon dan majalisar wakilai Farouk Lawan ya yi kan wani hukunci
- Hukuncin daurin na zaman gidan yarin ya biyo bayan samunsa da laifin karbar cin hancin dalar Amurka 500,000
- Tsohon dan Majalisar dai bai gamsu ba ya garzaya kotun daukaka kara inda aka rage zaman gidan yari daga shekaru bakwai zuwa
A ranar Juma’a ne kotun kolin kasar ta yi watsi da daukaka karar da tsohon dan majalisar wakilai Farouk Lawan ya yi kan hukuncin da karamar kotun ta yanke na daure shi.
Wata babbar kotun birnin tarayya ta yankewa Lawan hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin karbar cin hancin dalar Amurka 500,000 a lokacin da yake rike da mukamin shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar da ke binciken badakalar tallafin man fetur a shekarar 2012.
KARANTA WANNAN: AFCON 2024: Zakarun Kamaru Sun Isa Abidjan Don Karawa da Super Eagles
Alkaliyar kotun, Angela Otaluka, ta ce Lawan ya bukaci dala miliyan 3 kuma ya karbi Dala $500,000 daga hannun Femi Otedola a shekarar 2012 don cire kamfanin Otedola na Otedola, Zenon Oil and Gas, daga cikin sunayen kamfanonin da ake tuhuma da zamba a tsarin tallafin man fetur.
Ta kuma bayyana cewa Lawan na da laifuka uku da suka hada da cin hanci da rashawa.
Lawan bai gamsu ba ya garzaya kotun daukaka kara inda aka rage zaman gidan yari daga shekaru bakwai zuwa biyar.
Lawan yana gaban kotun kolin yana rokon kotun da ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke.
Da yake karanta hukuncin, mai shari’a Tijani Abubakar ya amince da hukuncin kotun daukaka kara tare da yin watsi da karar.
A wani labarin kuma, An Bai Wa Iyalan Jami’an da Suka Mutu Cekin N41m a Jigawa
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gabatar da cekin kudi har na sama da Naira Miliyan N41 ga iyalan Jami’an da suka mutu
An bukaci wadanda suka ci gajiyar kudin da su yi amfani da kudaden yadda ya kamata domin ci gaban su
Tuni wadanda Suka ci gajiyar kudaden Suka ce sun zo ne a daidai lokacin da ake daya dace kuma sun yi alkawarin yin amfani da su yadda ya kamata
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gabatar da cekin kudi har na Naira Miliyan (N41,527,360.37k) ga iyalai/yan uwa da abokan arziki na Jami’an da suka mutu a jihar Jigawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, AT Abdullahi, shine wanda ya mika cekin ga Iyalan jami’an ‘yan sanda guda ashirin da biyu (22) wadanda suka rasu a lokacin da suke bakin aiki a madadin babban sufeton ‘yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, a Headquarter rundunar da ke Dutse.