- Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya kafa kotunan tafi da gidanka guda biyar domin gurfanar da masu karya dokar tsaftar muhalli
- Kafa kotunan tafi-da-gidanka an yi shi ne da nufin aiwatar da dokokin muhalli da tsaftar muhalli a jihar
- Duk wanda aka kama da laifin karya dokar zai fuskanci fushin doka
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kafa kotunan tafi da gidanka guda biyar domin gurfanar da masu karya dokar tsaftar muhalli a duk wata.
Kwamishinan muhalli na jihar Dr. Nura Ibrahim Dandoka ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a lokacin tsaftar muhalli na wata-wata a Dutse babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN: Usman Ahmed Ododo Ya Zama Sabon Gwamnan Jihar Kogi
Ya ce an kafa kotunan tafi da gidanka a dukkan masarautu biyar da ke jihar da suka hada da, Hadejia, Gumel, Kazaure, Ringim da Dutse.
Kafa kotunan tafi-da-gidanka an yi shi ne da nufin aiwatar da dokokin muhalli da tsaftar muhalli a jihar.
Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci ‘yan majalisar zartarwa da ‘yan majalisar jiha wajen gudanar da ayyukan tsaftar muhalli.
Ya ce manufar tsaftar muhalli na wata-wata tana da manufar inganta tsaftar mutum da muhalli a jihar.
A wani labarin kuma, Gwamnan Kwara Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Kasafin Kudin 2024
Gwamnan Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya rattaba hannu kan kudurin kasafin kudi na shekarar 2024
Gwamnan ya bayyana cewa Hakan wani mataki ne mai karfin gwiwa na fadada ababen more rayuwa da bunkasa tushen tattalin arziki
Tuni gwamnan ya amince da kudurin dokar gyara kananan hukumomi ta jihar
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya rattaba hannu kan kudurin kasafin kudi na shekarar 2024 ya zama doka a ranar Juma’a.
Gwamnan yana mai cewa Hakan wani mataki ne mai karfin gwiwa na fadada ababen more rayuwa da bunkasa tushen tattalin arzikin jihar bisa tsari mai dorewa.