- Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta kame wata mai yiwa kasa hidima ta bogi mai suna Ogeh Bethel Chibuife
- An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel ya fitar
- Tuni wadda ake zargin tayi bayani dalla-dalla kan lamarin
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta kame wata mai yiwa kasa hidima ta bogi mai suna Ogeh Bethel Chibuife bisa laifin shiga sansanin Magaji Dan Yumusa Orientation Camp da ke Keffi, babban birnin jihar ba bisa ka’ida ba.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya fitar ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan bindiga sun yi awon gaba da taliya a Zariya
Nansel ya ce wanda ake zargin, wanda ta kasance dalibar karin shekara ce a fannin Hulda da Jama’a, daga Jami’ar Jihar Ebonyi, ta shiga sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC na kwana 21 da nufin gudanar da shirin batch A, Stream 1 na masu yiwa kasa hidima na 2024, kuma an gano ta ne a lokacin tantance yawan wadanda suke sansanin.
Ya ce wani jami’in NYSC ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a ranar Lahadi, kuma jami’an rundunar ne suka kama ta.
“Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin daliba ce a Jami’ar Jihar Ebonyi, Faculty of Management Science and Department of Public Administration.
Sannan ta furta cewa a shekarar 2022 ya kamata ta kammala karatunta, amma tana da kwasa-kwasan da ta gaza yin nasara da yawa, kuma a kokarinta na boye karyar da ta yiwa iyayenta, ta je kasuwa ta siyo rigar NYSC/wasu kayan da aka tanada na masu yiwa kasa hidima kuma ta shiga cikin sansanin don daukar hotuna da aika wa iyayenta kafin ma’aurata su same ta,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Kwastam Ta Cafke Haramtattun Kayayyaki Na N5.5bn a 2023 – Kakaki
Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen shiyyar C, Owerri ta ce ta kama wasu haramtattun kayayyaki da suka kai zunzurutun kudi har Naira biliyan 5.5
Hukumar tace a cikin lokacin da ake bitar, rundanar ta kwato tsabar kudi har naira miliyan 152 daga hannun masu shigo da kayayyakin
Ya kasance mafi girma a tarishin hukumar, idan ba zato ba tsammani ya kasance na farkon kama irin wannan nau’in haramtattun kayayyaki masu haɗari da kwayoyi masu ƙarfi
Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen shiyyar C, Owerri ta ce ta kama wasu haramtattun kayayyaki da suka kai zunzurutun kudi har Naira biliyan 5.5 tsakanin watan Janairu zuwa watan Disambar shekarar 2023.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Jerry Attah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.